Nafisa Abdullahi
Wannan suna ba boye yake ba a arewacin Nijeriya musamman ga wadanda suke da sha’awar kallon fina-finan Hausa, tsawon shekaru 10 da suka gabata Nafisa Abdullahi na daga cikin manyan jarumai mata da tauraruwarsu ke haskawa a wannan fanni na masana’antar Kannywood.
An bayyana Nafisa a matsayin jarumar da take da matukar kwarewa a kowane irin matsayi aka bata a cikin shirin fim musamman na tausayi ko kuma akasin haka, Nafisa ta fito a manyan fina-finan Hausa na Kannywood da suka hada da Lamiraj, Ya Daga Allah da kuma Sai Wata Rana wanda shi ne shiri na farko da ya haskakata a idon Duniya har aka santa a matsayin babbar jaruma a masana’antar Kannywood.
Rahama Sadau
Rahama Sadau ta zama kallabi a tsakanin rawuna idan aka zo maganar shirin fim a Nijeriya, inda ta zama jaruma ta farko da ta fito a cikin masana’antun fina-finai uku da suka hada da Kannywood, Nollywood sai kuma Bollywood na kasar Indiya kuma duk a cikin wadannan Rahama ta taka muhimmiyar rawar da ba kowace irin jaruma ce za ta iya takawa ba.
Rahama Sadau na daga cikin jaruman fina-finan Hausa da suke iya magana da yare daban-daban kamar Hausa, Turanci da kuma Indiyanci, hakan ya sa jarumar ‘yar asalin jahar Kaduna bata gamu da wani cikas ba a kokarin da take yi na shiga sassan Duniya domin ci gaba da harkar fim,daga cikin fina-finan Turanci da ta fito akwai Up North, Sons Of The Caliphate da kuma POSTCARDS.
Halima Atete
Wata jarumar Kannywood wadda sunanta ya karade koina a masana’antar Kannywood ita ce Halima Atete, ta zama daya tamkar dubu a lokacin da take cikin ganiyarta a masana’antar Kannywood, har ta kai ga lashe kyautar gwarzuwar jarumar Kannywood ta City People Entertainment Awards a shekarar 2013 bayan fitowarta a cikin shirin Dakin Amarya da Kona Gari.
Atete ta shahara a fina-finan Kannywood a shekarun 2010 zuwa 2017 inda ta fito a fina-finai fiye da 150, bayan harkar fim Halima tana da Gidauniyar da take taimaka wa masu karamin karfi haka zalika tana daga cikin jakadan hukumar kwallon kafa ta kasar Sifen (Laliga) tare da jarumi Ali Nuhu.
Maryam Booth
Maryam Booth ko kuma Dijangala kamar yadda aka fi saninta na daya daga cikin jarumai mata da suka shiga harkar fim da kafar dama, duk da cewar akwai ‘yan uwanta da suke shirin fim kafin ita ta shigo harkar, Maryam ta samu tagomashi yayin shigowarta masana’antar Kannywood inda ta samu dubban masoya tun bayan da ta fito a cikin shirinta na farko mai suna Dijangala inda anan ne ta samu wannan lakanin nata.
Bayan harkar fim Maryam tana harkar kwalliya da kwalisa, hakan ya sa ta bude shagon kwalliyarta da da radawa suna MBooth Beauty Parlour ,Dijangala na daga cikin jaruman masana’antar Kannywood da aka shaidesu da mutunta al’adar Bahaushe saboda irin suturar Hausawa da take sakawa a kowane lokaci.