Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya fitar da wani takardar bayani mai taken “Hada hannu wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya a kafar intanet”, wadda ta bayyana cewa, gina wannan al’umma a kafar intanet, na da matukar muhimmanci a zamanin da ake ciki.
A cewar takardar, bisa la’akari da saurin ci gaban da ake samu a bangaren fasahar sadarwa a duniya, hidimomin intanet sun shiga dukkan harkokin rayuwa da na ayyukan jama’a.
A don haka, jama’a na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro a kafar, abun da ya wajaba a hada hannu wajen shawo kansu.
Ta kara da cewa, al’umma mai makoma ta bai daya a kafar intanet, muhimmin bangare ne na ginin al’umma mai makoma ta bai daya a duniya.
Bugu da kari, takardar ta bayyana cewa, manufofi da shawarwarin da suka shafi ci gaba da tsaro da shugbanci da moriya ta bai daya, sun dace da manufofin samar da al’ummar duniya mai makoma ta bai daya da kuma siffofin kafar intanet, kana, inganta samun al’umma mai makoma ta bai daya a kafar intanet, za ta samar da karin kuzari ga fasahohin zamani, da tsaro mai karfi da kara fadada hadin gwiwa kan wannan batu. (Fa’iza Mustapha)