Akalla gine-gine takwas ne suka ruguje, makabarta ta nutse, mazauna gari da dama ba a gansu ba bayan an shafe sa’o’i uku ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Maiduguri da kewaye a jihar Borno.
Yankuna da dama kamar Bulumkutu, Damboa, Moduganari a Maiduguri, babban birnin jihar sun cika da ruwan saman, yayin da wata makabarta da ke Jajeri a karamar hukumar Jere ta jihar ta nutse, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin jama’a.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Neja
- Kwamitin Kolin JKS Ya Shirya Taron Bita Tare Da Wadanda Ba ’Yan Jam’iyyar Ba
Wani mazaunin Jajeri da bai ambaci sunansa ba a wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo, ya roki gwamnatin jihar Borno da ta kawo musu dauki domin shawo kan ambaliyar ruwan da ta yi barna a makabarta.
“Muna kira ga gwamnatin jiharmu da ta kawo mana agaji da gaggawa domin da yawa daga cikin kaburburan da ke makabartar, sun rufta bayan ruwan saman, wannan aikin ya fi karfin mu.” In ji shi.
A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yansandan jihar Borno ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da lamarin ya shafa.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar (PPRO), ASP Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a Maiduguri, ta ce rundunar ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da abin ya shafa.
Ya kuma tabbatar da cewa, “Abin takaici, gine-gine takwas sun ruguje amma ba a samu asarar rai ba.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp