Rahotanni daga Jihar Kano, sun bayyana yadda aka shiga fargaba yayin da wani gini mai hawa biyu da ya ruguje ya fada kan wasu magina da ake aikin gini a yankin Kuntau da ke karamar hukumar Gwale a jihar.
Wata majiya ta tabbatar wa Leadership Hausa cewa ginin ya rufta kan maginan da ke aikin fiye da 15.
- Da ÆŠumi-É—umi: An Kashe Babban Kwamandan Sojoji A Katsina
- Girman Darajar Manzon Allah (SAW) Da Allah Ya Yi Rantsuwa Da Ita (6)
Tuni dai masu aikin ceto suka fara zakulo mutanen da ginin ya rutsa da su.
Kawo yanzu dai an tabbatar da mutuwar mutum daya daga cikin mutane uku da aka zakulo, yayin da biyun ke cikin mawuyacin hali.
Sai dai ya zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga jihar, ko kuma adadin mutanen da suka rasu ko wadanda suka ji rauni.