Masu aikin ceto a Jihar Manipur a arewa maso gabashin Indiya na bincike domin gano mutum 20 da suka bace kwanaki bayan wata girgizar ƙlkasar mai karfi da aka yi.
Sama da mutum 40 ne suka mutu a girgizar kasar ya zuwa yanzu, wadda kuma ta lalata wani bangare na wata tashar jiragen kasa.
- Matsalar Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Hana Hakar Ma’adanai
- ‘Yan Daba Sun Yi Kokarin Kona Majalisar Dokokin Bauchi
Yawancin wadanda lamarin ya rutsa da su leburori ne da kuma ‘yan sa-kai na sojojin India.
Hukumoi sun ce mamakon ruwan sama da afkuwar wata girgizar kasa sun kawowa aikin ceto cikas.
Mamakon ruwan sama da aka yi ta tafkawa ya janyo ambaliyar ruwa a jihohi da ke arewa maso gabashin kasar musamman ma jihohin Assam da Manipur da Meghalaya da kuma Tripura.
Hakan ya kawo tasiri sosai a jihar Assam, inda sama da mutum 150 suka mutu sakamakon ambaliya da girgizar kasa da daidaita miliyoyin mutane.
An ceto mutum 18 da rai daga wajen da lamarin ya faru a karshen mako.
Sai dai jami’ai da ke wajen sun shaida wa ‘yan jarida cewa ‘ikon Allah’ ne kawai zai ceto mutane da yawa.