Masu aikin ceto sun bazama neman mutane sama da 60 da girgizar kasa ta rutsa da su biyo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, inda hakan ya janyo mutuwar mutane bakwai a Kudancin Ecuador.
Girgizar kasar wadda ta auku a daren ranqr Lahadi har ta kai wayewar Litinin, ta lalata gidaje da dama, inda kuma mutane 23 suka samu raunuka.
Wasu jami’ai sun ce, Iftila’in ya auku ne a kauyen Alausi da ke a gundumar Chimborazo.
Wani mai suna Manuel Upai mai shekara 40 kuma lebura ya shaida wa kafar yada labarai ta AFP cewa ‘yan uwansa biyar girgizar kasar ta danne su a karakshin kasa.
Kauyen na Alausi na mazauna kimanin 45,000 wanda kuma ya kasance yana zagaye da tsaunuka da bishiyoyi.
Girgizar kasar ta kuma lalata hanyoyi da makarantu da sauran wurare da ke kauyen.
An ruwaito wani mai suna Jose Agualsaca, ya ce da kyar ya samu ta kubuta daga girgizar kasar, inda ya ce, kusan ya tsallake rijiya da baya ne a cikin mintuna 15 yayin da yake kwashe kayansa daga cikin gidansa.
Shugaban kasar Guillermo Lasso a cikin sanarwar da ya fitar a Twitter, ya bayyana cewa, masu kashe gobara daga sauran yankuna sun garzaya zuwa kauyen domin taimaka wa al’ummar da iftila’in ya shafa.
Shugaban ya kuma yi kira ga mazauna kauyen da su fice daga kauyen, inda ya kara da cewa, gwamnatin kasar ta kuma umarci sauran hukumomin tsaro da na kiwon lafiya don su taimaka wa masu aikin ceton.
Shugaban ya kara da cewa, an kuma tanadi matsugunai na wucin gadi da za a ajiye wadanda iftila’in ya shafa.
Tun lokacin da aka fara girgizar kasar a wannan shekarar ruwan saman mai kamar da bakin kwarya a Ecuador ya janyo mutuwar mutane sama da 22 da lalata gidaje 72.