• English
  • Business News
Saturday, June 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gobara Ta Ƙone Wani Gidan Mai A Legas

by Sadiq
2 days ago
in Labarai
0
Gobara Ta Ƙone Wani Gidan Mai A Legas
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gobara ta tashi a wani gidan mai da ke kan titin Old Akute, a unguwar Obawole a Iju Ishaga, da ke ƙaramar hukumar Ifako-Ijaiye a Jihar Legas.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) ta tabbatar da afkuwar gobarar, wadda ta fara ne da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Laraba.

  • Yadda Kasar Sin Ta Zo Da Sabon Salon Zamanantar Da Sashen Jigilar Kayayyaki
  • Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Kaso Kusan 80% Sun Soki Musabbabin Barkewar Tarzoma A Amurka

Wasu shaidu sun ce sun ji ƙarar fashewa mai ƙarfi, wanda ya jawo hankalin mazauna unguwar da masu wucewa.

Jubril Gawat, mai bai wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu shawara kan kafafen sada zumunta, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce jami’an hukumar kashe gobara sun isa wajen cikin gaggawa.

Labarai Masu Nasaba

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Habaka Daga Manyan Tsare-Tsare Zuwa Matakai Na Ainihi

Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai

A cewarsa, gobarar na iya kasancewa ta samo asali ne daga wani gini da ke bayan gidan man.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar na iya tashi ne daga tankunan mai da ke ƙasa, kafin ta bazu zuwa cikin gidan man gaba ɗaya.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta yi gaggawar killace wajen domin hana cunkoso da tabbatar da tsaron jama’a yayin aikin kashe gobarar.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar, Shakiru Amodu, ya tabbatar da cewa an samu nasarar kashe gobarar kafin ta bazu zuwa gidajen da ke kusa.

Kafin ƙarfe 6 na yamma, jami’an agajin gaggawa sun shawo kan lamarin gaba ɗaya, tare da killace yankin da abin ya shafa domin kaucewa wata barazana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Gidan MaiGobaraLegas
ShareTweetSendShare
Previous Post

Zan Ci Gaba Da Ɓata Wa Masu Sukar Tinubu Rai Da Ayyuka – Wike

Next Post

Basaraken Da Aka Sace A Kogi Ya Kuɓuta Bayan Shafe Kwanaki 27 A Hannun ‘Yan Bindiga 

Related

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Habaka Daga Manyan Tsare-Tsare Zuwa Matakai Na Ainihi
Ra'ayi Riga

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Habaka Daga Manyan Tsare-Tsare Zuwa Matakai Na Ainihi

3 minutes ago
Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai
Labarai

Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai

4 hours ago
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Janye Taron Addu’ar Neman Wadatar Abinci
Manyan Labarai

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Janye Taron Addu’ar Neman Wadatar Abinci

5 hours ago
Tinubu
Labarai

Dimokuradiyya A Shekara 26: Ba Yabo Ba Fallasa

5 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci

6 hours ago
jam'iyyu
Rahotonni

Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya

19 hours ago
Next Post
Basaraken Da Aka Sace A Kogi Ya Kuɓuta Bayan Shafe Kwanaki 27 A Hannun ‘Yan Bindiga 

Basaraken Da Aka Sace A Kogi Ya Kuɓuta Bayan Shafe Kwanaki 27 A Hannun 'Yan Bindiga 

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Habaka Daga Manyan Tsare-Tsare Zuwa Matakai Na Ainihi

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Habaka Daga Manyan Tsare-Tsare Zuwa Matakai Na Ainihi

June 14, 2025
Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (1)

Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (1)

June 14, 2025
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)

Kula Da Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi

June 14, 2025
Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai

Gwamnati Ta Yi Barazanar Matakai Masu Tsauri Kan Masu Fasa Bututun Mai

June 14, 2025
Amfanin ‘Ya’yan Gwanda Da Yadda Ake Sarrafa Su

Amfanin ‘Ya’yan Gwanda Da Yadda Ake Sarrafa Su

June 14, 2025
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Janye Taron Addu’ar Neman Wadatar Abinci

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnati Ta Janye Taron Addu’ar Neman Wadatar Abinci

June 14, 2025
Tinubu

Dimokuradiyya A Shekara 26: Ba Yabo Ba Fallasa

June 14, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Addu’ar Kwana 3 Don Samun Isasshen Abinci

June 14, 2025
Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA

Kudaden Da Ake Karba A Kogin Hadejia Jama’are Daga Hannun Manoma, Ba Haraji Ba Ne – HJRBDA

June 14, 2025
Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025

Wani Gidan Gona A Jihar Ogun Zai Fitar Da Tarwada Ta Kimanin Naira Biliyan Shida A 2025

June 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.