Gobara ta kone gidan karamar ministar babban birnin tarayya Abuja, Dr Mariya Mahmoud Bunkure da ke Abuja ranar Lahadi.
Mai taimaka wa ministar kan harkokin yada labarai, Mista Austine Elemue, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, hukumomin da abun ya shafa na binciken musabbabin tashin gobarar.
- Waiwaye: Yadda Tsoffin Ministoci Suka Gina Babban Birnin Tarayya Abuja
- NLC Na Zargin Gwamnatin Nijeriya Da Shirya Kai Wa ‘Ya’yanta Hari Yayin Zanga-zangar Yunwa
Ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10:00 na safe a gidan da ke lamba 7 Roseline Ukeji Close, Mark Okoye Street, Asokoro, Abuja.
Da aka tuntubi mukaddashin daraktan hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya Abuja, Amiola Adebayo, ya ce hukumar ta samu wannan kiran ne da karfe 10:30 na safe, inda nan take ta tura ‘yan kwana-kwana zuwa wurin.
Adedayo ya ce duk da cewa ba a yi asarar rayuka ba, gobarar ta kone dukkan benan gidan mai dakuna 7.
Ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da ke ciki gidan da suka kone kamar gadaje da tufafi da takardu da kayan ado da sauran kayayyaki masu daraja.
Jami’in ya ce an shawo kan gobarar da misalin karfe 2:51 na rana, ya ya kara da cewa ana zargin wutar lantarki ce a dakin yara musabbabin gobarar.