Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da yunkurin tayar da hankali yayin da masu sayar da magunguna suka fara kwashe kayansu zuwa sabuwar kasuwa da ke Dangauro a jihar Kano.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Hussaini Gumel, ya shaidawa manema a Kano ranar Lahadi cewa an kama wadanda ake zargin ne sakamakon rufe bakin filazar Mai-Karami da ke kasuwar a Kano.
- NDLEA Ta Cafke Masu Safarar Kwaya 198, Sun Lalata Wurin Sayar Da Kwaya 21 A Kano
- Gwamnatin Tarayya Ga Masu Shagon Magunguna Da Aka Rufe A Kano : “Ku Koma Sabuwar Cibiyar Da Aka Gina”
Gumel ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da wasu ‘yan kasuwar ke kwashe kayayyakinsu zuwa sabuwar kasuwarsu da ke birnin Kano Economic City, dangwauro, a wajen birnin na Kano.
Ya bayyana cewa wasu ‘yan bata-gari sun yi yunkurin haifar da hargitsi a wurin, amma ba tare da bata lokaci ba ‘yan sanda suka tarwatsa su.
Ya ce, manufar wadanda ake zargin shi ne su yi awon gaba da kaya tare da kutsawa cikin wasu shaguna da ke Plaza.
Kwamishinan ya ce wadanda ake zargin yanzu haka suna hannun ‘yan sanda, ya kara da cewa ya bayar da umarnin bayar da “ tsaro a filin Filazar”.
Ya ce an tura karin jami’an ‘yan sanda domin samar da tsaron da ake bukata a yayin da ake ci gaba da jigilar kayayyaki zuwa sabuwar kasuwa.