Mutum 66 sun rasa rayukansu yayin da wata gobara ta tashi a wani Otal mai hawa 12 a Arewa Maso Yammacin Turkiyya.
Gobarar ta faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na tsakar dare a ɓangaren girki na Otal ɗin, lokacin da otal-otal ke cika saboda hutun tsakiyar zangon karatun ɗalibai.
- An Watsa Shirin Fadakarwa Na Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Masar
- Ana Sa Ran Bude Sabon Babin Raya Dangantakar Sin Da Amurka
Ministan Lafiya na Turkiyya, Kemal Memisoglu, ya ce mutum É—aya daga cikin waÉ—anda suka jikkata yana cikin mawuyacin hali, yayin da mutum 17 daga cikin 51 da suka samu raunuka aka sallame su daga asibiti bayan an duba lafiyarsu.
A lokacin da gobarar ta tashi, Otal ɗin na ɗauke da baƙi 234.
Rahotanni sun ce mutum biyu sun mutu yayin da suke ƙoƙarin tsallake ginin don tserewa wutar.
Ministan Cikin Gida na Turkiyya, Ali Yerlikaya, ya tabbatar da cewa mutum 51 sun jikkata a gobarar da ta ƙone Otal ɗin Kartal a lardin Bolu, wanda ke tazarar kilomita 300 daga birnin Istanbul.
Tuni gwamnatin Turkiyya ta naÉ—a kwamitin mutum shida don bincike kan musabbabin wannan gobara mai muni.
Ministan ya bayyana damuwarsa kan wannan babban rashi: “Mun rasa rayukan mutum 66 sakamakon wannan iftila’i.