Rundunar ‘yansandan kasar Sri Lanka, ta ce gidaje 80 ne suka lalace sakamakon wata gobara da ta tashi a wani yanki mai yawan jama’a a Colombo, inda mutane kusan 220 suka rasa matsugunansu.
A cewar rundunar ‘yansandan, gobarar ta tashi ne a yankin Kajeemawatte Flats da ke Thotalanga da misalin karfe 8 na daren daren ranar Talata kuma an dauki ma’aikatan kashe gobara na sa’o’i da yawa don shawo kan gobarar.
An tura motocin kashe gobara goma sha biyu.
- Kotu Ta Tabbatar Da Machina A Matsayin Dan Takarar Sanatan APC A Mazabar Yobe Ta Arewa
- Yadda Aka Yi Jana’izar Jarumin Kannywood, Umar Malumfashi
Kawo yanzu dai ba a samu asarar rai ba a lamarin, kuma wadanda abin ya shafa an ajiye su a cibiyoyi daban-daban da wuraren ibada.
Har yanzu dai rundunar ‘yansandan ba ta tantance musabbabin tashin gobarar ba, kuma ba a yi kiyasta asarar dukiyoyi da aka yi ba.
Shugaban kasar Ranil Wickremesinghe, ya umurci sakataren shugaban kasar, Saman Ekanayake da ya dauki matakin kai dauki cikin gaggawa ga daukacin mazauna yankin da gobarar ta shafa.