Wata mummunar gobara ta laƙume fiye da rumfuna 500 a Kasuwar Shuwaki da ke cikin ƙaramar hukumar Gari ta Jihar Kano, lamarin da ya jawo asarar dukiya mai tarin yawa ga ƴan kasuwar.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ce ta tabbatar da afkuwar gobarar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis.
- NUJ Reshen Kano Ta Taya Ahmed Mu’azu Murna Kan Naɗin Da NAHCON Ta Yi Masa
- Gobara Ta Tashi A Kasuwar Alaba Da Ke Legas
A cewar sanarwar, gobarar ta tashi ne a ranar Laraba, 22 ga Oktoba, da misalin ƙarfe 3:25 na rana, bayan samun kiran gaggawa daga Kwamandan tashar wuta ta Gari, Abdulmalik Muhd, wanda ya sanar da ofishin kashe gobara na Dambatta wacce ta tura jami’ai zuwa wurin da abin ya faru.
“Da jami’anmu suka isa wurin, sun tarar da wani fili mai fadin kafa 3,000 da 2,500 wanda ke ɗauke da rumfuna kimanin 1,000. Daga cikinsu, rumfuna 529 ne suka ƙone ƙurmus,” in ji Abdullahi.
Ya ƙara da cewa jami’an hukumar sun yi nasarar kashe gobarar kafin ta bazu zuwa sauran sassan kasuwar, kuma ba a rasa rai ba a lamarin. Rahotannin farko sun nuna cewa gobarar na iya zama sakacin wasu masu shan barasa da ke zama a kasuwar ne ya haddasa ta.













