Da safiyar yau Lahadi ne da misalin karfe 8:58 gobara ta tashi a wani kamfani da ake sarrafa sanadarai a cikin jihar Legas.
Gobarar ta tashi ne a wani daki da ake adana kwalaben lemon kwalba.
Daraktan hukumar kashe gobara da bayar da dauki na jihar Adeseye Margaret ya ce, jam’ian kashe gobara daga yankin Ikeja, Alausa da Bolade sun samu nasarar kashe gobarar don karta yadu zuwa sauran dakunan adana kayan kamfanin.
Jami’in hukumar bayar da agajin gaggauwa ta kasa reshen jihar, Ibrahim Farinloye ya tabbatar da tashin gobarar.
Ya ce, tun da farko ma’aikatan kamfanin suma sun taimaka wajen dakile yaduwar gobarar, inda ya ce, bayan da masu kamfanin suka iso kamfanin, sun bayar da umarnin a fasa kofofin dakin da ake adana kayan, wanda in bad an haka, da ba za a iya shawo kan gobarar ba.
NEMA ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi taka tsan-tsan kan tashin gobara don kaucewa yin asara.