Gobara ta lalata wata haramtacciyar ma’ajiyar man fetur a Yola babban birnin jihar Adamawa.
Gobarar ta tashi ne da yammacin Laraba da ke gefen wata shahararriyar mahadar Maidoki, kusa da kofar shiga filin tashi da saukar jiragen sama na Yola, Jimeta.
- Yawan Tsofaffi Masu Sama Da Shekaru 60 A Sin Da Suka Karbi Alluran Rigakafin COVID-19 Ya Zarce Miliyan 240
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Zai Yi Jawabi A Yayin Bude Taro Zagaye Na 2 Na Yarjejeniyar COP15
Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 6:30 na yamma, inda ba a tantance adadin man fetur din da aka ce wani babban dan kasuwar bayan fage ya saya ya ajiye a ma’ajiyar ba.
Baya ga rumbun ajiyar da abin da ke cikinsa, motocin da aka ajiye a kusa da wajen sun lalace sakamakon gobarar.
Gobarar dai ta ci gaba da ci har cikin dare kuma mazauna Yola sun gaza zaune sun gaza tsaye saboda gobarar.
Gobarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da karancin man fetur a fadin Jihar Adamawa, inda aka yi ta fama da tsadar man fetur din.
A safiyar Laraba a Yola, man fetur ana sayar da akalla kowace lita kan Naira 300 a kananan gidajen mai, yayin da ‘yan kasuwar bayan fage wato ‘yan bunburutu ke karbar Naira 1,700 zuwa Naira 2,000 kan kowane galan.