Gobara da ta tashi da daddaren ranar Juma’a ta lalata shaguna da kayan miliyoyin Naira a kasuwar Olusola Saraki, Ita-Amo, a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar, wadda ta fara ci tun misalin ƙarfe 9 na dare, ta shafi shagunan da ke ɗauke da kayan sawa, da naman kaza, da kayan masarufi.
Ma’aikatar kashe gobara ta jihar ta ce tashin gobarar ya faru ne sakamakon wutar lantarki mai ƙarfi da aka kawo daga kamfanin IBEDC.
- Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Legas Za Ta Kara Samar Da Kwararru – Kwamishina
- Sin Ta Kafa Kwamitin Kwararru Domin Kara Inganta Fasahar Kirkirarriyar Basira Ta AI
Mai magana da yawun ma’aikatar, Hassan Adekunle, ya bayyana cewa bayan ɗaukar matakin gaggawa na kashe gobarar, an samu nasarar ceto shaguna 269 daga cikin shaguna 276 da ke kasuwar. Sai dai shaguna 7 sun babbake, ciki har da waɗanda ke sayar da naman kaza, kayan sawa, da kayan masa rufi.