Sanata Muhammad Danjuma Goje mai wakiltar Gombe ta tsakiya a ranar Litinin ya kaddamar da shirin rabon buhunan takin NPK 12,000 ga al’ummar mazabar sa.
Sanatan ya ce ya bayar da takin ne kyauta ga al’ummar Mazabarsa ba tare da la’akari da wata Jam’iyyar Siyasa ba.
Goje wanda shi ne Shugaban Kwamitin Sufurin Jiragen Ruwa na Majalisar Dattawa, ya ce wadanda za su ci gajiyar tallafin sun hada da sarakuna da hakimai da dagatai da masu unguwanni da kungiyoyin mata da matasa da kuma manoma daga sassan kananan hukumomin Akko da Yamaltu/Deba na karamar hukumar Gombe ta tsakiya.
Ya yi bayanin cewa sarakuna biyar na Akko, Deba, Gona, Pindiga, da Yamaltu za su karbi buhu biyar kowannen su yayin da hakimai 74 na shiyyar za su karbi buhu uku kowannensu, sannan kowanne daga cikin dagatai 254 za su samu buhu biyu kowanne.
Goje ya kara da cewa, za a bai wa masu unguwanni 2,458 Buhu daya kowannensu yayin da za a raba buhu 10 ga kowace mazabu 874 da ke kananan hukumomin Akko da Yamaltu/Deba.