Gwamnatin Jihar Gombe ta cimma matsaya kan fahimtar juna tsakaninta da kamfanin sufurin jiragen sama na Rano Air Limited don fara zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci daga Abuja zuwa Gombe, a ƙoƙarin jihar na kyautata sufuri da zirga-zirga haɗi da kyautata kasuwanci.
Hakan ya biyo bayan ganawar da Gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi ne da manyan jami’an gudanarwan kamfanin a masauƙin Gwamnan da ke Abuja, inda ɓangarorin biyu suka ƙarƙare shirye-shiryen fara jigilar.
- Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu
- ‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe
Don tabbatar da haɗin gwiwar, ɓangarorin biyu sun sanya hannu kan wata yarjejeniya a hukumance, inda Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Jihar Gombe, yayin da Babban Manajan (ayyuka) na kamfanin na Rano Air, Mr Abah Godwin, ya rattaba hannu a madadin kamfanin.
Shugaban riƙo na Filin Jirgin Brig. Zakari Maimalari International Airport Gombe, Engr. Suleiman Daniel Musa, da Mista Auwal Sulaiman Ubale, su suka kasance shaidun ɓangarorin biyu.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, Kamfanin Rano Air zai riƙa turo jirginsa samfurin Embraer 145 mai ɗaukar fasinjoji 50 don jigila sau huɗu a mako daga Abuja zuwa Gombe, kana daga Gombe zuwa Abuja, musamman a ranakun Litinin, Laraba, Juma’a, da Lahadi, kamar yadda Babban daraktan yaɗa labarun Gwamnan Jihar Gombe, Malam Ismaila Uba Misilli ya sanar cikin wata sanarwa.
Tawagar kamfanin na Rano Air a wurin ganawa da gwamnan, ta haɗa da Babban Manajan (Ayyuka), Abah O. Godwin; da Accountable Manager Alhaji Lawal Sabo Bakinzuwo; da Shugaban Sashin Ayyuka na ƙasa Bashir Abdullahi Wudilawa; da Shugaban Sashin Bunƙasa Harkokin Kasuwanci na kamfanin, Auwal Sulaiman Ubale.
Jami’an kamfanin sun tabbatarwa gwamnan cewa kamfanin na Rano Air zai samar da nagartacciyar hidima abar dogaro, mai inganci kuma mai haba-haba ga kwastomomi, ta yadda za a samu sauƙin tafiye-tafiyen kasuwanci da bunƙasa harkokin tattalin arziki a faɗin jihar da Arewa Maso Gabas baki ɗaya.
“Gwamna Inuwa Yahaya ya yi maraba da wannan ci gaba, inda ya bayyana hakan a matsayin wata shaida kan yadda Jihar Gombe ke da zaman lafiya da kwanciyar hankali kuma jihar da ke maraba da harkokin kasuwanci,” sanarwar ta naƙalto.













