Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin GORON JUMA’A, shafin da yake bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa dana nesa, har ma da wadanda aka dade ba a haduwa.
Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishenku wadanda ku ka aiko mana da su kamar haka.
- Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin
- Xi Ya Taya Jami’ar Tianjin Murnar Cika Shekaru 130 Da Kafuwa
Sako daga Amina Idi Tanko daga Jihar Gombe:
Ina gaishe da mai gidana Mallam Babangida Bello Tanko, sai yarana Muhammad (Abbah), Bello (daddy) Sagir, Khadijah (Momi), Zainab (Zeezee\Abu). Sai ‘yan’uwana dake nan garin Gombe da Kano Kamar su; Malam Dan Lami, Hajja Fati (Maman Fiddau), Alhaji Mallam Bello Bebeji, da sauran wanda ban fada ba da fatan sun yi juma’a lafiya.
Sako daga Fatima Ibrahim Kofar Ruwa daga Jihar Kano:
Ina mika sakon goron juma’a na ga daukacin mutanena kamar kawata kuma aminiyata wato Kursiyya Sabo Bature dake Zaria, sai Mahaifiyyata Goggo Ladi, sai mahafina Baffah Chiroma.
Sako daga Ahmad Abubakar, Jihar Zamfara:
Dan Allah Leadership ina so ku mikamin sakon gaisuwata zuwa ga ubangidana Alhaji Sa’idu me Takalma dake Zamfara. Sai kuma masoyiyata Saddika Ibrahim dake Zamfara, sannan ina gaishe da abokaina irinsu; Yahaya dan small, Ashiru me takalma, Tijjani Baba, sai Sani Aminu, da sauran abokanmu da ban fado ba.
Sako daga Hassana Habib Garba, Jihar Katsina:
Sakon gaisuwar farko zan fara da mijina, ina gaishe da mijina abin kaunata kuma uban ‘ya’yana har karshen rayuwa in sha Allah wato Mubarak Muhammad Isah. Sai kuma iyayena su ma ina gaishe su, ina gaida kannena, da kuma kawayena.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp