Jama’a barkanku da wannan rana ta juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A, shafin da ya ke bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa da na nesa, har ma da wadanda aka dade ba a hadu ba.
Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishen da ku ka aiko mana, inda sakon farko ya fara da cewa;
- Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4
- Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe
Sako daga Baffa Halluru Jihar Gombe:
Dan Allah Leadership ina so a mika min sakon gaisuwa ta zuwa ga kakana Isah Baffa, da kuma mahaifina Halluru Isah, da mahaifiyata Lauratu, sannan ina mika sakon gaisuwar juma’a zuwa ga abokaina irin su; Yusufu, Garbati, Dan’asabe, Zulyadaini, Lurwanu, Isma’ilu, da takwara na baffa dan Inna, da fatan sakona zai isa gare su.
Sako daga Saifullahi Bilyaminu Jihar Jigawa:
Ina gaishe da Arsenal Star, ina gaishe da maza dubu, ina gaishe da Auwal, da Abdulsalam, ina gaishe da Aminu ba ka karya, ina gaishe da yellow me jimuna, da ‘yan club din mu gabadaya.
Sako daga Anwar Bin Isma’il Jihar Jigawa:
Assalamu Alaikum. Ina gaishe da masoyiya ta Zainab Tahir, tare da kannena Habiba, Karima, Aisha, Idris, da yayana Ibrahim da kuma Anti na Haj. Bilkisu.
Na gode.
Sako daga Fatima Lawan Jihar Katsina:
Ina gaishe da Momina abar kaunata kuma abar alfahari na Hajiya Hadiza, sai kuma mahaifina Alhaji Lawan A Basu Kala, ina gaishe da kawata Laila Kamal, da Zuwaira Jibrin, da Binta Sa’ad, da Lubabatu Isah, da sauransu kawayena wadanda ban ambato su ba, duk ina gaishe su da al’ummar musulmi gabadaya, da kannena da yayyena.












