Barkanku da juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A. Shafin da ke bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki, na kusa dana nesa. A yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishen wanda ku ka aiko mana da su, inda sakon ya fara da cewa:
Sako daga Zahra Ibrahim Jihar Kaduna:
Ina gaida Ummina Hajiya Saratu da Abba na Alhaji Ibrahim, ina gaida yayata Zainab da kannena Usman da Mustapha da Mai sunan Ummi, da fatan sun yi sallar juma’a lafiya.
Sako daga Aliyu Haider Tijjani daga Jihar Gombe:
Gaisuwar Goron Juma’a zuwa ga abokanaina Umzzy boi da Yaro dan yayi, ina gaida Auwal dan gaske da Lawan Liman (Double eL), da sauran abokan karatuna da ban fado ba. Ina gaida bebina, masoyiyata abar kaunata Maryama ‘yan mata. Da fatan za su yi sallar juma’a lafiya.
Sako daga Iklima Ahmad Jihar Kaduna:
Ina gaida bebin bebi abin alfaharina, mijina uban ‘ya’yana daga ni ba wata in sha Allah, da fatan zai yi juma’a lafiya. Sannan ina gaida iyayena da iyayensa da fatan su ma za su yi juma’a lafiya, sannan ina gaida kawayena na ko ina, ina gaida kannena da yayyena dukkamsu da fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Amina Yahaya Jihar Kano:
Da farko ina gaida iyayena su ne sahun farko, sannan ina gaida Yayyena da kannena, ina gaida kawayena na islamiyya da boko, ina gaishe da kannen mamana da yayyen mamana dukka ina gaishe su, da fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Mujtapha Nasir Jihar Katsina:
Ina gaida gidan Jaridar Leadership Hausa gaba daya ma’aikatanta, ina gaida iyayena da ‘yan uwana baki daya, ina gaida rabin raina, abar sona, farin cikin raina Zulaihat Isma’il da fatan za ta yi kwalliyar juma’a me kyau irin wadda ta saba yi.