Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin Goron Juma’a, shafin dake bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa dana nesa har ma da wadanda aka dade ba a hadu da su ma.
Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishenku da ku ka aiko mana, inda sakon farko ya fara da cewa:
Sako Daga Fauziyya Umar Sahabi
Ina mika gaisuwata zuwa ga mijina Abdulhamid da ‘ya’yana Absulbasit Abdulhamid da Farouk Abdulhamid, Allah ya yi muku albarka. Sannan ina mika gaisuwata zuwa ga kanwata Suhaila da kanina Abdulsalam. Kazalika ina mika gaisuwa ta zuwa ga makociyata Maman Nihat, ina kuma gaida anty Khadija, Allah ya kara miki lafiya
Sako Daga Alkazim Garba
Ina mika gaisuwa na zuwa ga iyaye na da kanwata Fatima da kanina Hussaini, da yayana Mahadi da yayana Isiyaku da matarsa Hanifa da aboki na Zola da kuma budurwa ta Bintu, da abokan aikina Dabid , Sadik , Lillian da kuma Zarah.
Sako Daga Safiyya Abdulhamid
Ina mai mika sakon gaisuwa ga al’umm’a, da jami’an tsaro, da kuma shuwagabaninmu. Allah ya kara mana hakuri da juriya baki daya. Kuma Allah ya hada kowa da rabonsa a duniya
Sako Daga Rufa’i Salihu
Ina mika gaisuwa na ga iyalina Zainab da dana Haliru da kuma mahaifiyata Baba Kande da mahaifina malam Salihu da kanina Yahuza, Allah ya jikan inna Karima, Allah ya bamu hakurin rashin ta. Allah ya kawo mana saukin rayuwa amen.
Sako daga Hayatu musa mohammed
Ina mika gaisuwata zuwa ga mahaifiyata, da mahaifina da kanina da kuma matata. ina mika gaisuwata zuwa ga abokan aikina Ado , Rashad, Zakari da kuma Rabiu.