Jama,a barkammu da juma,a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma,a. Shafin da ke bawa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa. A you ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan anyi sallar juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar juma’a tare da kaiziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka.:
Sako daga Abubakar Tijjani:
Assalaikum alaikum!
Al’umar musulmi, ina yiwa kowa fatan alkhairi tare da fatan anyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyaye na da ina musu fatan alkhairi da fatan sunyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayu na da kanne na da fatan sunyi sallar juma’a lafiya. Ina gaida yayu iyaye na da kannan su tare da yi musu fatan anyi sallar juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da juma’a.
Sako daga Isah Aliyu
Ina mika sakon goron jumma’a ga alumman musulmi gaba ki daya, da jamia’an tsaro dake kasan nan baki daya. Ina mika gaisuwa na ga mahaifiya ta hajiya lamee musa, da mahaifina alhaji Aliyu Isah.Ina mika sakon gaisuwa na ga yaya ta ummi, da kanwa ta Aisha ,da yaya na faisal, da kanina Abdulrahman, da yaya na sadik. Da fatan sako na ya iso ku cikin koshi. Lafiya.
Sako daga Bilkisu Maharazu
Ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga iyayena da fatan alkhairi ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida dana waje da fatan sun yi sallar juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukakin musulmi tare da fatan an yi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.