Jama’a barkanku da kasance wa tare da wannan shafi na Goron Juma’a, shafin da yake mika sakonnin gaishe-gaishenku zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa dana nesa, wanda kuka aiko mana da su. Godiya da fatan alkhairi ga daukacin jama’ar da ke, kasance wa da wannan shafi na Goron Juma’a, fatan alkhairi ga daukacin jama’ar da ke tare da mu a ko da yaushe. Sakon gaisuwa ta musamman ga dukkanin ‘yan uwana baki daya tare da gaisuwa ta musamman ga Editana Abdulrazak Yahuza Jere, ina yi muku fatan alkhairi da fatan za ku yi Juma’a Lafiya, da fatan kuma za ku sha ruwa lafiya. Ga kadan daga cikin sakonnin da aka turo kamar haka:
Sako daga Hamisu Bature Jihar Sokoto:
Ina yi wa al’ummar musulmi barka da wannan rana ta juma’a sannan ina yi wa kowa fatan samun nasarar wannan wata da muke ciki na ramadan, da fatan kowa zai sha ruwa lafiya. Ina gaida mata ta Hadiza Nuhu, ina gaida amaryata wadda za ta zo nan gaba in sha Allah Maimuna Sadauki. Ina gaida abokaina Isyaku Abbas, Hassan Ilyasu, Muttaka jibrin da sauran ‘yan majalisan mu duk ina gaishe su da fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Amatullahi Nasir Jihar Katsina:
Ina gaida Masoyina farin cikin zuciyata Yusuf Aja magana, ina gaida Iyayena da sauran ‘yan uwana kamar su Anti Karima, Anti Hafsa, Yaya Hassan, da Yaya Shamsu, ina gaida kannena kamar su Zainura, Amina, Sa’adatu, Aisha da fatan sun yi juma’a lafiya da fatan za su sha ruwa lafiya.
Sako daga Nura Hassan Jihar Gombe:
Ina gaida abokina Isah asha kwana, da Hamza Haruna (H2) mai takaddu, ina gaida ubangidana kuma babban yaya Alh. Aliyu Gwani, ina gaida dukkanin ‘yan uwa musulmi fatan za su sha ruwa lafiya.
Sako daga Hadi Tsohon Sarki Daura 08164205067:
Ass. Gaisuwar goron juma’a zuwa ga mai girma subeb ciyaman na jahar katsina Alh. Lawal Buhari da shugaban ilimin Firamare na karamar hukumar Daura Alh. Nura Lawal da shugaban matasa na APC na jahar katsina Alh.. Murtala Shehu da Malam Yasir Lawal Buhari da Abdulhakim Lawal Buhari da Alh. Buhari Lawal Buhari da ofisa Lawal Buhari da Usman Lawal Buhari da Adamu Lawal Buhari Baban Anti da Sulaiman lLawal Buhari da Alh Sa’idu Lawal Buhari da fatan za su yi juma’a lafiya. Goron Juma’a ga Hon.Fatihu Muh da Hon.Yusif Shehu Ratiyos da Hon. Bala da Hon. Ibrahim da Alh Ali Haruna da Hon. Abdulmalik Mu’azu da fatan za su yi juma’a lafiya. Gaisuwar goron juma’a ga mai girma Fada da Aljani Badadi Hon. Fatihu muh da Hon. Shehu Abdu da Hon. Bala Ibrahim da Hon. Yuusif Shehu Ratiyos da Hon. Abdulmalik Mu’azu da Mal. Aliyu Sabo da fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Fatima Hakeem Jihar Kaduna:
Ina gaida iyayena da kannena, da yayye na, ina gaida masoyina wanda ya kawon Ramadan Basket Aliyu farin gani, ina gaida Kawata Eysho da Maimu da Khadija da takwarata Zahra Dagwas, ina gaida Hajjaju ‘yar gidan Baba Tijjani, ina gaida Auwal yaron kirki da Isma’il da dukkanin kannena ina gaida su da ‘yan sikul din mu da fatan za su sha ruwa lafiya.