Jama’a barkan mu da wannan rana ta juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A, shafin dake bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa dana nesa har ma da wadanda aka dade ba a hadu ba.
Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da sakonnin gaishe-gaishen da ku ka aiko mana kamar haka;
- Sin Ta Bai Wa Habasha Kayayyakin Tallafin Jinya
- Mun Shirya Fuskantar APC Domin Ceto Talakawa – Abubakar Malami
Sako daga Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), Jihar Kano:
Ina isar da sakon gaisuwa ga ‘yan ‘AUA TECHNOLOGIES’ bakidaya da kuma group na ‘lunchpad’ bakidaya, kamar su; Dr Sunusi, Mommy, Maryam Yahaya Gambo (MYG Soft drink) Kofar Ruwa,
sai kuma M. Abdurashid caps da Sammani da kuma bakidaya mutanen ‘AUA TECHNOLOGIES’ Kofar Dawana’u, da fatan za su yi juma’a lafiya.
Sako daga Haj. Aisha Rilwan Jihar Bauchi:
Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga ‘Yan uwana Haj. Marka, da Salamatu Rilwan, da Khadija da Hafsat. Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga kawayena Hadiza Jibril, Haj. Sadiya, Abida Ahmad, Zuhriyya Aminu, Suwaiba Sauban da sauran kawayena duk a garin Bauchi.
Sako daga Ahmad Halliru Jihar Katsina:
Ina gaida masoyiyata, abar kaunata, muradin zuciyata Leemat Beauty, sakon na musamman ne zuwa gare ta abar alfahari na. Ina gaida abokaina Sulaiman me inkiya, Fauwaz na Azima, Faisal dan boi, Masoyi me jama’a, Safiyanu J.k, dan Adamawa, Bello yaron kirki, da duk jama’ar AZ Group.
Sako daga Aisha Imam Gwarzo Jihar Kano:
Ina gaida kawata Fatima Kamal, Yayana Ishak, kanwata Khadijah, Sadiyya, Khairat, Tally, Nusaiba, Hafsat Ameer, Zainab Haruna, Jamila Hassan da fatan sun yi juma’a Lafiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp