A wannan makon mun kawo muku tattaunawar da wakiliyarmu Bilkisu Tijjani Kasim ta yi da wata ‘yar kasuwa mai neman na kanta, mai suna Zainab Adam Abdullahi. Ta bayyana yadda ta tsuduma harkokin kasuwanci da irin alfanun da take samu a ciki. Ga dai yadda hirar ta kasance.
Da farko masu karatu za su so sanin cikakken sunanki da tarihinki
Assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu.
Da farko dai ni sunana Zainab Adam Abdullahi Durumin Iya Kano, na yi Firamare a Masallaci Special Primary School, sannan na yi Sikandire a sabuwar Kofar Koki a can na gama karatuna zuwa S. S. S 3.
Shin Zainab matar aure ce?
Eh ni matar aure ce, na yi aure bayan na gama Sikandire na yi aure, Allah ya azurta ni da haihuwa na hayayyafa Alhamdulillah, matakin karatuna iya Sakandire kuma Alhamdulillah na gode Allah komai yana tafiya dai-dai, sannan kuma ina da burin inda na tsaya ‘ya’yana su wuce wannan wajen, kuma Alhamdulillah Allah ya cika min wannan burin nawa yana ma kan cika min su a yanzu da nake miki magana ‘ya’yana biyu suna karati a Jami’a.
Malama Zainab ‘yar kasuwa ce ko kuma ma’aikaciya ce?
A’a ni ba ma’aikaciya ba ce, bayan na yi aure daga baya kuma na fada dan saye da sayarwa a hankali a lokacin a yanzu za’a yi shekara goma zuwa sha biyar haka.
Wanne irin kasuwanci kike yi?
A lokacin da na fara sana’a ta kin san yadda rayuwa take, tufafi nake sayarwa, ina sai da kayayyaki a lokacin zan je kasuwa na sayo yadiika da shaddodi da atamfofi na sayo su ina kawo wa, idan na bubbugawa masu saya gidana zai cika da mutane za a zo masu saya su saya wadanda kuma da kaina zan kai musu na kai musu to, tafi-tafi sai ya kasance yadda tsadar yanayin rayuwa yake ya zo ya kasance shi tufafi bako da yaushe ake sayensa ba daga nan sai na koma kayan abinci kamar irin su shinkafa, wake, su manja duka irin wannan duka ina siyarwa idan kana son buhu zan dakko maka idan kuma kwano-kwano kake so duka zan dakko maka ina ma dan taba kayan a yanzu halin da nake ciki a haka nake sai kasuwancin online da na hada nake yi na sai da kome da mutum yake so idan yana so zan dakko na kawo masa a bayar a kai masa ko ina yake amma a gidana de kayan abinci ba wanda bana sayarwa.
Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwancin?
A gaskiya ba abin da ya ja hankalina nake wannan kasuwancin har na fara sana’a da a wajen mijina ni kadai ce kuma falillahil hamdu komai yana yi min ya yi wa ‘ya’yana a da a lokacin to daga baya da muka zama mu biyu sai na ga a cikin bukatun alal misali kamar guda biyar za’a maka uku a bar ka da biyu sai na ga wannan zama bai same ni ba dole kai ma sai kai yi hubbasa saboda kar ka tagayyara kai da ‘ya’yanka to dalilin abin da yajawo hankalina kenan har na fara sana’a wani abin ba.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
Abin da yake faranta min rai kamar idan ina da bukata idan abokin zamana bai min ba ni na yi wa kaina ina jin dadi sosai ina yi wa kaina abin da in Allah ya huwace min ina biya wa kaina bukatata da ta ‘ya’yana to idan na tuna da wannan na kan ji dadin sana’a ta.
A da can da kike karama mene ne burinki?
To a lokacin da nake karama gaskiya ina da burin yin karatu har gaba da sikandire Allah dai bai sa zan yi ba amma yanzu ma Alhamdulillah.
Dame kike so mutane su rinka tunawa dake?
Ina so mutane su tuna da ni akan halina na gaskiya da rikon amana ba yabon kai ba saboda duk wanda ya bani amana in sha Allahu ina kokrin rikewa kuma karyar mutum ya ce na tona masa ita to ina so mutane su rinka tunawa da ni da wannan.
Wanne irin addu’a ne idan aka yi miki kike jin dadi?
Addu’ar da idan aka yi min nake jin dadi ita ce idan mutane suka sai kayana a online na tura musu ya isa gare su suka kirani suce ya iso na gode Allah ya saka da alkhairi Allah ya sa kifi haka to ina jin dadin wannan addu’ar.
Wanne irin goyon baya kika samu daga wajan mijinki?
Alhamdulillah gaskiya ba ni da matsala da mijina wajen sana’a ta.
Kawaye fa?
Alhamdulillah Allah Ubangiji ya bani kawaye, kawayena suna rufa min asiri da kaunar juna babu hassada ba komai sai dai idan mutum yana cikin matsala in Allah ya yarda za su fito da kai ina da wadannan kawayen ina da na wadanda suke na zahiri kuma ina da na waya na online, kuma ni na online sun fiye min na zahiri saboda iya kauna tsakani da Allah suke yi min da wadanda suka zo gare ni muka hadu da wadanda ma ba su zo ba ba abin da zan ce musu sai dai Allah ya saka da alkhairi. Sannan gaskiya na dade ina gwagwarmaya ban taba samun wani tallafi ba sai kwanan nan ba da jimawa ba wajejan Azumi na samu tallafi daga wata baiwar Allah da ta dubi Allah ta dubi Annabi ta tallafa min wannan baiwar Allah ba zan taba mantawa da ita ba ta yi min taimako babban taimako da ba zan iya mantawa da ita ba sai de na ce Allah ya saka mata da Aljannar Firdaus, tun da na fara sana’a in aka cire yayana da ya fara bani jari to sai ita da ta tallafa min akan sana’a.
A karshe wace irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Shawarata ga ‘yan ‘uwana mata ita ce a rike gaskiya ban da cin amana ban da karya in za ka so mutum kuma ka daure ka so shi don Allah ba don komai ba ko don wani abinsa ba in dai mata za mu rike wannan to za mu zauna lafiya a tsakanin mu in sha Allahu gaskiya dokin karfe ka rike ta.