A ranar Talata ne ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Zimbabwe ya gudanar da bikin bayar da gudummawa a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, wanda ya farantawa marayu da sauran yara marasa galihu a kasar.
Yaran daga gidan marayu na Hupenyu Hutsva da ke karkarar Harare sun samu kyautukka da suka haÉ—a da barguna, abinci da kayan rubutu. Wannan gudummawar wani bangare ne na wani shiri na kiwon lafiya ga yaran Afirka, mai taken “A faranta zukatan yara: Aikin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka,” wanda uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta Æ™irikiro tare da hadin gwiwan kungiyar matan shugabannin kasashen Afirka ta raya kasa.
Tawagar likitocin kasar Sin dake kasar Zimbabwe sun kuma gudanar da gwaje-gwajen lafiya kyauta ga yara kimanin 100 bayan bikin.
A jawabin da mataimakiyar ministar harkokin kananan hukumomi da ayyukan jama’a Marian Chombo ta karanta a madadin uwargidan shugaban kasar Zimbabwe Auxilia Mnangagwa, ta nuna jin dadinta ga Peng bisa wannan tallafin. (Mai fassarawa: Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp