• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Guguwa Za Ta Sa Kasashen Sin Da Afirka Su Kara Rike Hannayen Juna

by Sulaiman
5 months ago
Sin

Idan yakin ciniki ya kasance guguwar da Amurka ta tayar a duniya, to hakan zai sa Sin da Afirka su kara rike hannayen juna.

A yau, an gudanar da taron ministocin masu kula da yadda ake aiwatar da sakamakon da aka samu, a dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, a birnin Changsha na kasar Sin. A wajen taron, an gabatar da sanarwar ta Changsha game da hadin gwiwar Sin da Afirka a kokarin tabbatar da hadin kan kasashe masu tasowa.

  • Tsohon Ɗalibi Ya Kai Hari Makarantarsu A Austria, Ya Kashe Ɗalibai 9
  • Tinubu Ya Ceto Nijeriya Daga Faɗawa Matsin Tattalin Arziƙi – Gwamna Namadi

Za a iya cewa, sanarwar hadin gwiwa ce da Sin da Afirka suka fitar a madadin daukacin kasashe masu tasowa, domin nuna kin amincewa da ra’ayin kashin kai, da yadda ake kashin dankali a duniya. A cikin wannan sanarwa, Sin da Afirka sun yi nuni da cewa, “rikicin da ake fama da shi a duniya, na samun ra’ayin kashin kai, da na kariyar ciniki, da cin zarafin wasu kasashe a fannin tattalin arziki, ya haddasa babbar matsala ga dimbin kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka”, tare da yin kira ga dukkan kasashe, musamman Amurka, da su koma kan turbar da ta dace ta yin shawarwari, da musayar ra’ayi kan sabanin ra’ayi a fannin ciniki.

Wannan sanarwar ta kunshi tofin Allah tsine ga yakin harajin fito, da yakin ciniki da Amurka ta kaddamar. Saboda kasar Sin da kasashen dake nahiyar Afirka da dama sun samu ‘yancin kai ne bisa yaki da ‘yan mulkin mallaka, da na mulkin danniya. Saboda haka tarihin gwagwarmaya ya ba su kwarin gwiwar tabbatar da adalci da kare mutunci. Ban da wannan kuma, a yayin da ake fuskantar cin zarafi na tattalin arziki da Amurka ke yi, Sin da Afirka ma suna da kwarin gwiwar hada karfi da karfe don samun nasara a fafutukar da suke ta kare moriyarsu.

Wannan kwarin gwiwa, da farko ya fito ne daga yadda kasar Sin ta mayar da martani ga yakin ciniki da kasar Amurka ta kaddamar. Bayan da kasar Sin ta samu tsokanar harajin kwastam mafi tsanani da Amurka ta saka mata, kasar Sin ba ta tsoro, kuma ba ta ja da baya ba, maimakon haka ta yi amfani da tsauraran matakan karbar karin haraji fito kan Amurka, da na hana fitar da wasu ma’adinai masu muhimmanci, don tilastawa Amurka komawa teburin tattaunawa. Ta haka, an baiwa duniya damar fahimtar halayyar “mai zalunci” da ke son nuna karfin tuwo, amma a hakika shi ma zai ji tsoro, idan a nuna masa karfi, da kwarin gwiwar da ake da shi.

LABARAI MASU NASABA

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

Don haka, a cikin sanarwar da aka fitar a wannan karo, kasashen Afirka sun nuna yabo kan jajircewar kasar Sin, da kuma kudurin da kasar ta dauka na kare adalci, da kuma ingancin tsare-tsaren tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa. Har ila yau, kasar Sin ita ma ta nuna godiya ga kasashen Afirka, kan yadda suke bin ka’idojin kare ‘yancin kai, da adalci, tare da tsayawa kan matsaya guda wajen fuskantar matsin lamba da aka sanya musu.

Hakika idan mun tantance kwarin gwiwar Sin da Afirka, za mu ga da farko ya zo daga dangantakarsu mai dorewa ta hadin gwiwa da juna. Za mu iya daukar misalin bangaren ciniki: daga shekarar 2000, lokacin da aka kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, zuwa bara, yawan ciniki tsakanin Sin da Afirka ya karu daga dalar Amurka biliyan 13.92 zuwa dalar Amurka biliyan 295.56, wanda ya karu da fiye da sau 20. Kana kasar Sin ta kasance abokiyar ciniki ta Afirka mafi girma a duniya tsawon shekaru 16 a jere. Sa’an nan, a watanni hudu na farkon bana, darajar ciniki tsakanin Sin da Afirka ta kai dalar Amurka biliyan 103.1, adadin da ya karu da kashi 8.1% bisa na makamancin lokacin bara. Kana idan mun duba nan gaba, a cikin wasikar taya murna ga taron da aka gudanar a birnin Changsha, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, za a aiwatar da shirin ba da damar yafe harajin fito 100% ga kasashe 53 dake nahiyar Afirka masu huldar diflomasiyya da kasar Sin, kana a sa’i daya kuma, zai samar da karin sauki ga kasashe mafin karancin tattalin arziki a Afirka don su fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin. Wadannan alkaluman da na ambata sun nuna cewa, daga a baya har zuwa yau, da kuma nan gaba, hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da Afirka na kara habaka. Wannan ya nuna yadda amintattun abokan hadin gwiwa ya kamata su kasance tare da juna.

Ko ta yaya wasu kasashe ke tayar da hankali a duniya, za mu iya ganin wannan hoto: Sin da Afirka, aminai na kwarai, suna tsayawa tare da juna, rike da hannayen juna, a kokarin tabbatar da ci gaban kasashensu na bai daya. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani
Ra'ayi Riga

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

October 27, 2025
Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ra'ayi Riga

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Next Post
Manchester City Ta Kammala Daukar Rayan Cherki Daga Lyon

Manchester City Ta Kammala Daukar Rayan Cherki Daga Lyon

LABARAI MASU NASABA

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

October 28, 2025
JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

October 28, 2025
An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025
Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

October 28, 2025
Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

October 28, 2025
Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe

October 28, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin

October 28, 2025
Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260

October 28, 2025
An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas

October 28, 2025
Gwamna Bago Ya Amince Da Biyan Karin Albashin Naira 20,000 Ga Ma’aikata 

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.