ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Ceto Nijeriya Daga Faɗawa Matsin Tattalin Arziƙi – Gwamna Namadi

by Sadiq
1 year ago
Tinubu

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziƙi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi musamman cire tallafin man fetur da sauya farashin dala sun ceci Nijeriya daga faɗawa cikin mummunan halin kuncin tattalin arziƙi. 

Ya ce ko da yake matakan sun fara jefa talakawa cikin wahala, amma yanzu haka suna samar da kuɗaɗen shiga da ake amfani da su wajen ci gaban ƙasa.

  • Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatun Akpabio Kan Dakatar Da Sanata Natasha
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Kogi Ta Gargadi Siyasantar Da Kalubalen Tsaro A Jihar

A cewar Namadi, Jihar Jigawa ta yi amfani da ƙarin kuɗaɗen shiga wajen gina sababbin hanyoyi sama da 47, gyara asibitoci fiye da 200, da kuma ɗaukar sabbin malamai da dubban ma’aikatan lafiya.

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa harkar noma, samar da ruwa da walwalar al’umma sun inganta sosai sakamakon waɗannan kuɗaɗe, lamarin da ke sauƙaƙa rayuwar talakawa.

Gwamnan ya kuma ce bunƙasa da Naira ke samu a halin yanzu yana taimakawa wajen daidaita tattalin arziƙin ƙasa da jawo hankalin masu zuba jari.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

A cewarsa, shuwagabancin Tinubu ya gina tubalin ci gaba mai ɗorewa ta hanyar yanke hukunci masu wahala amma masu amfani.

Dangane da sauyin jam’iyyun siyasa da ke faruwa, Namadi ya ce yawaitar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC alama ce da ke nuna yadda jama’a ke ƙara amincewa da shugabancin Tinubu da kuma burin da yake shi ga ƙasar nan.

Ya ce masu barin jam’iyyunsu suna haka ne domin suna ganin makoma mai kyau a ƙarƙashin jagorancinsa.

Har ila yau, Namadi ya bayyana cewa ziyarar aikin da ya kai Indiya kwanan nan ta samar da muhimman yarjejeniyoyi da masu saka jari da ƙwararru don bunƙasa harkar noma a Jihar Jigawa.

Ya ce an cimma matsaya a fannoni irin su kiwon shanu, kiwon kaji da samar da ingantattun iri, wanda zai ƙara samar da ayyukan yi, tsaro na abinci, da kuma ɗora Jigawa zuwa cibiyar noma ta ƙasa.

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Nijeriya Ta Fuskanci Cikas Wajen Karɓo Rancen Dala Biliyan 5 Daga Saudiyya

Nijeriya Ta Fuskanci Cikas Wajen Karɓo Rancen Dala Biliyan 5 Daga Saudiyya

LABARAI MASU NASABA

Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.