Babban darektan gidan talabijin na kasar Guinea-Bissau Amadu Djamanca ya bayyana cewa, kasar Guinea-Bissau na fatan zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin don ciyar da masana’antar watsa labaru gaba da kara daukaka muryarta a dandalin duniya.
Djamanca ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Bissau, babban birnin kasar, inda ya ce, kasar Sin na sa kaimi ga bunkasuwar muryoyin kasashen Afirka kan yanayin duniya, tare da baiwa kafofin watsa labaru na Afirka damammaki wajen ba da labaransu.
- Matakin Sanya Karin Harajin Kwastam Ba Zai Daidaita Matsalar Da Amurka Ke Fuskantar Ba
- NDLEA Ta Gargadi Iyaye Kan Bayyanar Alawar Ƙwaya A Kano
Kazalika, ya bayyana fatan karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, ta hanyar musayar shirye-shirye, da horar da jami’ai, da yin amfani da kwarewar kasar Sin wajen karfafa sanin makamar aiki na kwararrun ma’aikatan kafofin watsa labaru na kasar Guinea-Bissau.
Ya kara da cewa, kafa hadin gwiwa na dogon lokaci tare da kafofin watsa labaru na kasar Sin, zai taimaka wa kasar Guinea-Bissau wajen nuna al’adunta a dandali mai girma, da baiwa karin Sinawa damar sanin labaran kasar.
Ya ce, sabanin wasu kasashen yammacin duniya da ke yunkurin cusa wa Afirka dabi’unsu, Sin na daukar matakai na daban. Kasar Sin tana mutunta ‘yancin kasashen Afirka, tana kiyaye ka’idar samun moriyar juna, kuma ba ta sanya sharudda na siyasa. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)