A daidai lokacin da Nijeriya ta shiga sahun sauran kasashen duniya wajen bikin ranar ma’aikata ta duniya, yana da matukar muhimmanci mu yi nazari a kan hakki da gwagwamaryar ma’aikata a Nijeriya zuwa yanzu. Ranar ba wai ana nufin kawai a bayar da hutu ba ce a kuma yi fareti da bukukuwa kawai ba ne, ranar ce ta duba gudummawar ma’aikata da sadaukarwar da suka yi wajen gina kasa kuma gashi suna ci gaba da bayar da gudummawar ganin kasa ta samu ci gaban da ake bukata.
Ya kamata al’umma su fahimmaci cewa, ranar ma’aikata ko kuma kamar yadda wasu ke kiranta da suna ‘May Day’ ya samo asali ne daga kungiyoyin gwagwarmayar nema wa ma’aikata hakkokinsu. Ranar ta samo asali ne daga kasar Amurka a karni na 19 tun daga wancan lokaci kuma ake bukukuwan ranar a fadin duniya gaba daya.
- Sin: Kasashen G7 Suna Wakiltar Sabawa Ka’idojin Kasa Da Kasa
- Wasu Ke Neman Bata Mana Suna Kan Rikicin Shugabancin APGA – INEC
A Nijeriya an fara bikin ranar ne a shekarar 1980, bayan da gwamnatin soja ta Janar Olusegun Obasanjo ta ayyana ranar a matsayin ranar hutu.
A tsawon shekaru, ma’aikatan Nijeriya sun yi gwagwamarya daban-daban ta neman hakkokinsu wadanda suka hada da hakkin kafa kungiya da hakkin nemawa kansu hakkokinsu a kungiyance, da hakkin kariya daga cuttutuka a wajen aiki da bukatar a samar masu da mafi karancin albashi don su samu gudanar da aiki a cikin kwanciyar hankali.
Amma kuma a ra’ayin wannan jaridar har zuwa yanzu ba dukkan ma’aikatan Nijeriya ke amfana da wadannan hakkokin ba, da yawa daga cikin ma’aikatan Nieriya na ci gaba ne da fuskantar matsaloli da suka hada da rashin albashi mai inganci da kuna yadda ake nuna masu bambanci da kuma yadda suke aiki a cikin yanayi mai cutar da rayuwarsu.
Tabbas batun mafi karancin albashi shi ne lamari mafi girma a cikin matsalolin da ma’aikata suke fuskanta a Nijeriya. Jihoji da dama sun kasa biyan albashin ma’aikata. Wani rahoto na wata kungiya mai zaman kanta mai suna BudgIT, ta bayyana cewa a shekarar da ta wuce akawai jihohi 12 daga cikn jihohi 36 da muke da su na kasa akalla sun kasa biyan ma’aikata albashin daya ko biyu, wasu jihohin ma bashin da ma’aikata ke bin su na albashi da ya wuce na wata 6 wasu na bin bashin albashin fiye da shekara 3.
Wannan kuma yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu gwamnanoni ke kaddamar da wasu manyan ayyukan da babu yadda za a iya yinsu suna kuma zartar da kasafin manyan kudaden da za a rinka biyansu bayan in sun yi ritaya, ba za mu amince da wannan lamarin ba.
Gwamnatin tarayya na shirin cire tallafin man fetur wanda hakan kuma zai kara tsawalla tsadar kayan masarufi da harkokin rayuwar yau da kullun ta al’umma, a kan haka ne ya dace, gwamnati mai jiran kama madafun iko ta Bola Hamed Tinubu ta kara wa ma’aikata albashi tare da sauran abubuwan da za su rage radadin da za a shiga sakamakon cire tallafin man.
Wannan jaridar ta nuna kyamarta a kan yadda kungiyoyin ma’aikata ke shiga yajin aiki daga an samu wata takaddama, muna kuma godiya ga gwmanatin tarayya a kan yadda ta fara cika wa ma’aikatan alkawurransu, a ra’ayinmu, rajin aiki ya zama wani tsohon yayi, ya kuma kamata gwamnatin tarayya ta tabbatar da tana cikia dukkan alkawarin da ta dauka a tsakaninta da kungiyoyin kwadago a kowane lokaci.
Babu tantamamr cewa, babbar matsalar da ma’aikatan Nijeriya ke fuskanta a wannann lokacin ita ce ta rashin tabbas a wurin ayyukansu. Ma’aikata da dama a bangaren kamfanoni masu zaman kansu ana daukar su ne ba a tsarin dindindin ba, basu da wani tsari na taimaka wa rauyuwar su bayan sun ajiye aiki, kamar tsarin fansho da inshorar lafiya, wanda hakan yana cutar da rayuwarsu bayan sun tsufa sun ajiye aiki.
Wata matsalar da ma’aikata Nijeriye ke fuskanta ya hada da yadda ake nuna masu bambanci, musamman bambancin da ake nuna wa mata. Mata na cikin kaso mafi yawa na ma’aikatan Nijeriya amma suna fuskantar barazana da tsagwama a wuraren aikinsu.
Duk da wadannan kalubalen, ma’aikata a Nijeriya na ci gaba da fafutuka neman hakokkinsu ta hanyoyoin kungiyoyin NLC da TUC, sun ci gaba da gwagwarmayar nema wa ma’aikata hakkokinsu da suka hada da albashi mai tsoka da yanayin aiki mai kyau ba tare da takura ba, sun kuma taka rawar gani a kokarin yaki da nuna bambaci a tsakanin mata, ta yadda kowa za iya aiki a cikin walwala ba tare da fargaba ko wata takura ba.
Ya zama dole mu ci gaba da mutumtawa tare da tuna gudummawar da ma’aikata suka bayar a wajen tabbatar da mutuncin ma’aikata a fadin duniya.