An haifi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a cikin shahararren gidan a Jihar Legas da ke Nijeriya. Tinubu ya fara karatun makarantar firamare ta St. John a Aroloya da ke Jihar Legas, kuma ya ci gaba a makarantar Children Home da ke Ibadan a kudu maso yammacin Nijeriya.
Ya tafi kwalejin Richard Daley a Chicago, Illinois. A can ya nuna fajinta sosai wanda ya shiga cikin jerin zakakuran dalibai. Bayan haka, ya tafi jami’ar Jihar Chicago da ke Illinois, inda ya sami digiri na farko a fannin kasuwanci da kula da harkokin kudade.
A lokacin da yake karatun digiri na farko, ya sami lambar yabo ta zakakuran dalibi da lambar yabo ta malaman jami’a da kuma takardar shaidar karramawa a fannin kula da harkokin kudade.
A lokacin samartakansa, Tinubu ya kasance a cikin jerin sunayen shugabannin dalibai ya sami lambar yabo tare da samun tallafin karatu na jami’a da kuma takardar shaidar yabo a fannin lissafi da kudi a lokacin da yake kwaleji. Ya kuma samu lambar yabo ta musamman, saboda yana da GP 3.54 daga cikin 4.0.
A shekararsa na karshe a Jami’ar, Tinubu ya tsaya takarar shugabacin kungiyar dalibai kuma ya yi nasara. Wannan shi ne zabensa na farko a siyasa, kuma ya nuna yadda ya samu nasara a makaranta.
Bola Tinubu ya fara aikinsa ne a kasar Amurka bayan ya kammala karatunsa da ya samu karramawa da kyaututtuka da dama. Ya yi aiki da kamfanoni irinsu Arthur Anderson, Deloitte Haskins da Sells da GTE Serbice Corporation, wanda shi ne Babban Kamfanin Sadarwa na kasar Amurka.
Mahaifiyar Tinubu, Abibatu Mogaji, ta rasu ne a ranar 15 ga watan Yunin 2013, tana da shekaru 96. A ranar 31 ga Oktoban 2017, dansa Jide Tinubu, ya mutu sakamakon bugun zuciya a lokacin da yake Landan.
Gwagwarmayar Siyasar Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu ya zabi ya sadaukar da rayuwarsa wajen gudanar da aikin gwamnati. Ya shiga siyasa a karon farko a matsayin dan jam’iyyar Social Democratic Party (SDP). An zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai a mazabar Legas ta yamma.
Ya zama dan majalisar tarayya a shekarar 1992. Ya yi kaurin suna a majalisar dokoki ta kasa, inda ya jagoranci kwamitin majalisar dattawa kan harkokin banki da kuma kudade.
Ya shiga sahun mutane na gaba-gaba saboda darajar da ya samu a cikin harkokin siyasa.
Bayan juyin mulkin ranar 17 ga watan Nuwamba a Nijeriya a shekarar 1993, wanda ministan tsaro Sani Abacha ya yi, ya bar kasar.
Bayan ya dawo daga gudun hijira a shekarar 1998, ya yi saurin murmuruwa wanda aka zabe shi a matsayin gwamnan Jihar Legas a watan Mayun 1999. Ya shahara wajen kafa kananan hukumomi 37 a fadin jihar. Ya yi shekara takwas a matsayin gwamna.
Tinubu ya yi alkawarin gina gidaje 10,000 ga marasa galihu a lokacin da ya hau mulki a watan Mayun 1999, amma hakan bai faru ba. A cikin shekaru takwas da ya yi yana gwamnati, ya kashe makudan kudade a harkar ilimi a jihar tare da rage yawan makarantu ta hanyar mika da yawa daga cikinsu ga masu su domin ci gaba da kulawa da su. Bugu da kari kuma, ya gina sabon titin da ke da matukar muhimmanci saboda yawan karuwar jama’ar jihar cikin hanzari.
A watan Afrilun 2003, aka sake zabar Tinubu a matsayin gwamna tare da sabon mataimakin gwamna mai suna Femi Pedro. A wancan zabe, jam’iyyar PDP ta lashe kowace jiha a kudu maso yamma. Ya fafata da gwamnatin tarayya, wacce a lokacin take karkashin mulkin Olusegun Obasanjo, kan batun ko Jihar Legas na da hurumin kafa karin kananan hukumomin domin daukar dimbin al’ummarta. Gwamnatin tarayya ta kwace kudaden da aka tanada na kananan hukumomin jihar a sakamakon faruwar lamarin. Ya shiga cikin rigingimun da ake fama da shi da shugabannin PDP kamar Bode George, shugaban PDP na kudu maso yamma, da Adeseye Ogunlewe, tsohon sanata daga Jihar Legas wanda aka nada ministan ayyuka a lokacin rabin wa’adinsa na mulki.
Femi Pedro, mataimakin gwamnan ya bayyana muradinsa na tsayawa takarar gwamna, lamarin da ya janyo takun-saka tsakanin Tinubu da Pedro. A jajibirin zaben fid da gwani na jam’iyyar, Pedro ya janye kudirinsa na tsayawa takarar gwamna a AC a zaben 2007. Ya rike mukamin mataimakin gwamna amma ya koma jam’iyyar Labour Party.
A ranar 29 ga Mayu, 2007, wa’adin Tinubu a matsayin gwamnan Jihar Legas ya zo karshe lokacin da dan takarar jam’iyyar AC, Babatunde Fashola ya karbi mulki. A cikin 2009, Tinubu ya shiga tattaunawa da jam’iyyun badawa don hada kan na samar da jam’iyyar daya tilo da za ta iya yin gogayya da jam’iyyar PDP wadda ke kan karagar mulki a lokacin. Bayan hadewar jam’iyyun ACN, CPC, ANPP, wani bangare na APGA da kuma wadanda suka kafa sabuwar PDP (nPDP), zuwa jam’iyyar APC a watan Fabrairun 2013, Tinubu na daya daga cikin ‘yan siyasa da dama da suka kirkiro jam’iyyar APC.
Tinubu A Matsayin Uban Siyasar Jihar Legas
Jama’a da dama na kiran Tinubu “Ubangidan Legas”. A wani fim na 2015, mai suna ‘The Lion of Bourdillion,’ ya nuna gaskiyar lamari game da mulkin siyasa da kudi na Tinubu a kan jihar, ya nuna yadda ya gudanar da mulkin jihar ba tare da dogaro da gwamnatin tarayya ba.
Tinubu ya kai karar furodusoshi da AIT, a kan Naira biliyan 150 domin bata masa suna, kuma an dauke fim din a kafafan sada zumunta a ranar 6 ga Maris, 2015. Duk da haka, yana da tarihin yin kamun kafa da wadanda suka gaje shi. Misali, a cikin watan Disambar 2009, an samu rahotannin cewa Fashola da Tinubu sun yi fada a kan sake zaben Fashola a 2011, inda Tinubu ya fi son Muiz Banire a matsayin kwamishinan muhalli. Kuma a 2015 makamancin wannan fada ya faru kan wanda zai maye gurbin Fashola. Tinubu ya hau kansa ne saboda yana goyon bayan Akinwunmi Ambode. Ambode ya zama magajin Fashola, amma Tinubu ya kawar da shi ya sanya Babajide Sanwo-Olu mai ci.
An zabi Bola Ahmed Tinubu a matsayin Sanata mai wakiltar Legas ta yamma a shekarar 1993. Ya kuma zama Gwamnan Jihar Legas daga 1999 zuwa 2007. Ana yi masa kallon daya daga cikin manyan ‘yan siyasar Nijeriya. Shi ne babban jigo na jam’iyyar APC na kasa.
Fitowar tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, ko shakka babu nasara ce.
Tinubu ya doke wasu mutane 13 masu neman tikitin tsayawa takara a zaben fid da gwani na jam’iyyar APC. Ya samu kuri’u 1,271, yayin da babban abokin hamayyarsa, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya samu kuri’u 316. Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya zo na uku da kuri’u 253.
Tinubu na daya daga cikin mutane 23 da aka amince da su shiga zaben fid da gwani da aka gudanar a Abuja daga ranar 7 zuwa 8 ga watan Yuni.
Kafin a fara kada kuri’a a zaben fitar da gwanin na jam’iyyar APC, bakwai daga cikin ‘yan takara 23 sun fice daga takarar, inda suka bayyana goyon bayansu ga Tinubu, yayin da daya kuma ya goyi bayan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo. Bugu da kari, wani mai neman tsayawa takara ya sauka amma bai bayyana goyon bayansa ga wani daya daga cikin abokan takararsa ba. Sakamakon haka, 14 ne kacal daga cikin 23 suka fafata a zaben fid da gwani.
Jerin wakilai 2,203 ne aka amince su kada kuri’a ga ‘yan jam’iyyar APC a zaben fitar da gwanin, wanda aka zabo daga kananan hukumomi 774 na Nijeriya.
Har ila yau, da yawa daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC da ke ganin Tinubu ne ya fi kowa cancanta a cikin ‘yan takarar da za suka fafata da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a babban zaben 2023.
Sai dai gwamnonin jihohin arewa na jam’iyyar APC sun dage sai mulkin ya koma kudu bayan shekaru takwas na Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya kasance dan arewa, wanda hakan ya yi tasiri da Tinubu ya samu nasarar lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar.
Darasi Daga Cikin Gwagwarmayar Rayuwar Tinubu
• Jajircewa da kuma rashin yin kasa a gwiwa wajen yakar abin da aka yi imani da shi, zai iya daukar lokaci kadan ko kuma da yawa wajen fuskantar tsanantawa na fafatuka, amma a karshe idan ana fafutukar neman gaskiya za a cimma nasara.
• Bai wa kai nasara a duk lokacin dab aka kudiri cimma manufa ba tare da tunanin wata matsala ba.
• Yin aiki tukuru kuma ka da a bar wata kofa ta lalaci wurin kasala duk abin da ake yi. Kirkiri dubarar harkokin kasuwanci da duniya ta amince da shi, domin samun damar habaka harkokin kasuwancinka.
• Hakuri da juriya da kuma tanadin abubuwan da ake kokarin cimmawa a kai.
Tinubu Ya Samu Kashi 25 A Jihohi 30, Wanda Ya Samu Kuri’a Miliyan 8.8
A halin da ake ciki kuma, da sanyin safiyar ranar Laraba ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC aka bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
A cewar INEC, Tinubu ya samu kuri’u 8,794,729, sannan ya samu kashi 25 a jihohi 30 wanda da hakan ne ya doke abokin takararsa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ya zama na biyu da kuri’u 6,984,520, sai Peter Obi na jam’iyyar LP wanda ya samu kuri’u 6,101,533.
Sashi na 134 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999, ya tanadi cewa za a bayyana wanda ya samu nasarar lashe takarar shugaban kasa ne kawai idan ya samu yawan kuri’u da aka kada a zabe, sannan kuma dole ya samu kashi daya bisa uku na yawan kuri’un da aka kada a zabe a kalla kasha biyu bisa uku na dukkan jihohi ciki har da Babban Birnin Tarayya wato Abuja.
Karamin sashe na 3 na wannan sashe ya bayyana cewa “idan ba a zabi dan takarar da ya dace daidai da sashe na (2) na wannan sashe ba za a yi zabe na biyu”.
Tinubu na da jan aiki a gabansa, sakamakon matsaloli da a yanzu haka suka yi wa Nijeriya katutu. Akwai ce-ce-ku-ce a kan abubuwan da Nijeriya ke bukatar kafin ta dawo kan hayyacinta.
A yanzu haka dai Nijeriya na fama da matsaloli da suka hada da tabarbarewar takardun naira, cire tallafin man fetur, hauhawar farashin kayayyaki, hauhawar, matsalar taro basussuka, yawaitar matasa masu zaman kashe wando da dai sauran manyan matsaloli. Babban abin da ke da muhimmanci shi ne, matsalar rashin tsaro da Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gabo ya yi kokarin ragewa ta hanyar fatattakar Boko Haram daga yankunan da ta kama a baya, amma har yanzu ana ci gaba da samun tarzoma a sassa da dama na Nijeriya.