A kokarin gwamnatin Jihar Bauchi na toshe kafofin sata da handame dukiyar al’ummar, ta kirkiro wata hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai suna ‘Bauchi State Public Complaints and Anti-Corruption Commission’ wanda tuni aka sanya mata hannu domin ta fara aiki gadan-gadan.
Da yake sanya hannu kan kudirin dokar bayan da majalisar dokokin jihar ta kammala bitarsa tare da amincewa da shi, gwamna Bala Muhammad, ya ce an samar da kudirin ne domin tabbatar da dakile masu yin zagon kasa ta hanyar cinye dukiyar al’umma daga cikin ma’aikatan gwamnati, ‘yan siyasa da kuma al’umma a fadin jihar.
- Ambaliyar Ruwa: Ya Dace Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Shinkafa – Dan Sa’a
- Gidauniyar Masari Ta Tallafa Wa Marasa Karfi A Jihar Katsina
Ya nanata cewar hukumar za ta samu cikakken ‘yancin gudanar da aikinta ba tare da yi mata katsalandan daga gwamnati ba, kana ya kuma tabbatar da cewa ba an kafa hukumar ne domin ta musguna wa abokan adawarsu a siyasa ba ne, illa domin tsarkake jihar daga harkokin cin hanci da amsar rashawa ta fannoni daban-daban.
A cewarsa: “Gwamnatin jihar Bauchi ta kwaikwayi sauran jihohi wadda dokar Nijeriya ta basu dama su fito da ma’aikatun da za su taimaka wajen sarrafa gwamnati da dakile cin hanci da rashawa da sama da fadi da dukiyar al’umma.
“Ba tare da cin mutuncin mutane ba, ba tare da sanya siyasa a ciki ba wajen yaki da rashawa ba.”
“Shi ya sa muma muka je muka duba dokoki har muka yi wannan kudirin dokar tare da tura wa majalisar dokokin jiha domin dubawa da tantancewa.
“Hukumace wacce ta samu asali daga yanayin da Nijeriya take, muna kara yin yawa kuma akwai bukatar hana wadannan munanan al’adu da dabi’u na cin hanci da rashawa a cikin al’umma,” ya fada.
Gwamna Bala, ya nuna cewa hukumar za ta taimaka sosai wajen saurin duba kesa-kesan rashawa lura da cewa hukumomin Gwamnatin tarayya irin su EFCC da ICPC suna nasu kokarin amma samar da wannan hukumar zai taimaka matuka wajen gudanar da kesa-kesai tun daga matakin farko.
Gwamnan ya ce hukumar za ta kasance ne kamar sauran hukumomin yaki da hancin hanci da rashawa wacce za a mata cikakken tsarin gudanarwa da daukan ma’aikatan da suka dace, ya kuma ce za su fara ne da nada manyan jami’an hukumar da za su jagoranci tafiyar ta da ita, “mutane masu gaskiya da adalci za mu nemo. Kuma za mu tabbatar an baiwa hukumar cikakken ‘yanta domin ta gudanar da aikinta a kashin Kai ba tare da ana shiga mata aiki ba. Ba Musguna ma wani ko wasu za a yi ba, amma so muke a tabbatar da gaskiya wajen gudanar da harkokin gwamnati.”
Bala Muhammad ya kuma ce samar da hukumar wani karin nasara ne ga gwamnatinsa. Sai ya jinjina wa Majalisar dokokin Jihar bisa gaggauwa sanya hannu kan dokar bayan da suka fahimci tasirin da za hakan zai yi ga cigaban jihar.
Tun da farko Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Sulaiman, ya ce a watan da ta gabata ne aka aike wa Majalisar kudirin Kuma Nan take suka zauna domin bita da yin abubuwan da suka dace a kai har ta kai ga sun amince da dokar.
Mataimakinsa Danlami Kawule ne ya wakilce shi a wajen sanya hannun, ya ce sun duba alfanu da muhimmanci kudirin ne ya sanya suka amince da shi.