Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa majalisar dattawan Kano (KEC) a matsayin majalisar bayar da shawara ga gwamnatin jihar Kano.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.
- Kotun Koli Ta Tabbatar Da Abba Kabir Yusuf A Matsayin Zababben Gwamnan Kano
- Shari’ar Kano: Kanawa Na Farin Ciki Kan Nasarar Abba A Kotun Koli
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa Allah ya albarkaci jihar Kano da dimbin dattijai da tsofaffin shugabanni da suka kai kololuwa a fannonin rayuwa ta fuskoki da dama.
Majalisar Dattawan ta kunshi tsofaffin Gwamnoni da Mataimakan Gwamnoni da Shugabannin Majalisar Dattawa da Shugabannin Majalisar Wakilai da Shugabannin Majalisar Jiha da Mataimakan Shugaban Majalisar da Alkalan Kotuna da suka yi ritaya da Sakatarorin Gwamnatin Jiha, da Tsoffin Shugabannin Ma’aikatan Jiha wadanda dukkansu ‘yan asalin jihar Kano.
Kazalika, majalisar ta hada da shugabanni al’umma da Malamai da ‘yan kasuwa da sarakunan gargajiya da tsofaffin shugabannin hukumomin tsaro na jihar Kano da sauran manyan dattawan da gwamnati za ta tantance tare da nada su.
Gwamnan ya jaddada cewa wadannan dattijai suna da tarin ilimi da hikima da gogewa don haka gwamnatinsa za ta nemi yin amfani da kwarewarsu.
Haka kuma gwamnan ya ce nan ba da jimawa ba za a tantance ranar da za a kaddamar da majalisar ta dattawan.