Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya fice daga jam’iyyar PDP.
Mai magana da yawunsa, Mallam Olawale Rasheed ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Litinin cewa Adeleke ya fice tun a ranar 4 ga wannan Nuwamba, 2025.
- Sin Ta Yi Kira Ga Japan Da Ta Gyara Kalaman Kuskure Tare Da Dakatar Da Kaucewa Gaskiya
- An Kaddamar Da Taron Fahimtar Kasar Sin Na Kasa Da Kasa Na Shekarar 2025
Ya aike da wasiƙar murabus ɗinsa ga shugaban jam’iyyar na Gunduma ta 2 a Ede ta Arewa a jihar.
Adeleke ya ce ya fice daga jam’iyyar ne saboda rikicin shugabanci da ke faruwa a jam’iyyar.
Ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi ya zama Sanata da kuma gwamna.
Akwai rahotannin da ba a tabbatar ba cewa yana iya komawa jam’iyyar Accord yayin da zaɓen gwamnan Osun na 2026 ke gabatowa, kasancewar PDP na fama da rikice-rikecen cikin gida.














