Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa.
Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar, ya samu fitowar masu zaɓe sosai tare da ingantaccen tsaro. Gwamna Adeleke ya yaba da yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana, inda ya buƙaci al’umma su ci gaba da kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ko matsin lamba ba.
- Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke
- An Yanke Wa Mutane 5 Hukuncin Kisa Bayan Sun Kashe Wani Bafullatani A Jihar Osun
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kaɗa ƙuri’arsa, ya jinjinawa hukumar zaɓe ta Jihar Osun (OSSIEC) bisa shirya ingantaccen zaɓe. Ya kuma jaddada muhimmancin dimokuraɗiyya a matakin ƙananan hukumomi, yana mai kira ga ‘yan jihar da su fito kwansu da kwarkwata domin amfani da hakkinsu na zaɓe.