Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya nuna matuƙar ƙaduwa da samun labarin rasuwar Manjo Janar Muhammadu Sani Sami (mai ritaya), Sarkin Zuru da ke jihar Kebbi kuma tsohon gwamnan tsohuwar jihar Bauchi a zamanin mulkin soja, wanda ya rasu a ranar Lahadi yana da shekaru 82 a duniya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Gwamnan ya ce, “Dukkanin abinda muka samu daga Allah ne, haka ma wanda muka rasa, sai dai mu miƙa komai gare shi domin samun dacewa. Mun wayi gari da rasuwar shugaba, uba, jagora kuma abin koyi, tsohon gwamnan jiharmu ta Bauchi a mulkin soji, kuma mai martaba Sarkin Zuru, Manjo Janar Sani Sami (rtd).”
- Kasashen Sahel Na Bukatar Agaji Domin Yaki Ta’addanci -Rasha
- Tattakin Arba’in: Muna Farin Ciki Da Yadda Gwamnati Ta Fahimci Ayyukan Mu Na Addini – Ahlul-Baiti
Gwamnan ya ƙara da cewa (Baba) Sami ya mulki jihar Bauchi daga 1984-1985 lokacin mulkin soji ƙarƙashin marigayi Janar Muhammadu Buhari, ya kuma yi ƙoƙari gaya, wajen assasa taswirar gina sabuwar jihar Bauchi (roadmap).
A saƙon ta’aziyya da ya fitar a ranar Lahadi ɗauke da sanya hannun babban hadiminsa a ɓangaren hulda da ‘yan jarida, Kwamared Mukhtar Gidado, gwamnan ya misalta marigayin a matsayin babban jigo, uba, dattijon kwarai, sarki mai daraja wanda ya bada gagarumin gudunmawa wajen hidimta wa ƙasar nan cikin gaskiya, riƙon amana da tsoron Allah.
Ya lura kan cewa tsohon gwamnan tsohuwar jihar Bauchi a lokacin da take haɗe da Bauchi da Gombe ya taka rawa sosai wajen aza tunanin ci gaban jihar wanda har jihar ta kawo yanzu cikin nasara.
Ya ƙara da cewa lallai za a jima ba a mance irin gudunmawar da marigayin ya bayar a ɓangaren aikin soja da hidimar da ya yi a mulkinsa na farar hula.
“A zamaninsa ya yi mulki cikin gaskiya, janyo kowa a jika, tabbatar da adalci da daidaito a ɓangaren jagoranci,” gwamnan ya shaida.
Gwamnan ya ƙara da cewa hatta a lokacin da ya ke Sarkin Zuru, Manjo janar Sami ya ci gaba da ɗabbaka halayensa ta kwarai, himmatuwa wajen hidima wa jama’a, son jama’a, jin ƙansu da tausayinsu a shugabancinsa a matsayin Sarki wanda ya yi cikin tsoron Allah.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa kura-kuransa kana ya sanya shi cikin aljanna maɗaukakiya. Ya kuma miƙa ta’aziyyasa ga iyalan mamacin, masarautar Zuru, gwamnatin jihar Kebbi, rundunar sojan Nijeriya, da ma al’ummar ƙasa bisa wannan babban rashin.
“A madadin ɗaukacin al’ummar jihar Bauchi, gwamnati da masu riƙe da sarautun gargajiya, dama dukkanin gwamnonin jam’iyar PDP, ina miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayi, Masarautar Zuru, gwamnatin jihar Kebbi da ma Daular Uthmaniyya kan wannan babban rashi, tare da addu’ar Allah yayi masa Rahama, da afuwa, da ba shi dacewa. Amin,” gwamnan ya shaida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp