Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya haramta wa ma’aikatan gwamnatin jihar amfani da motoci da kayan gwamnati wajen amfanin kansu ba a lokacin aiki ba.
Gwamna Buni ya bayyana hakan bayan ya rantsar da sabbin manyan sakatarorin guda 9, ranar Talata inda kuma ya bukaci su yi amfani da ilimi da basirarsu wajen inganta aikin gwamnati a ma’aikatun da aka tura su don ci gaban jihar.
Buni ya kara da cewa za a yi amfani da motocin gwamnati ne wajen ayyukan gwamnati kawai tare da bai wa sakataren gwamnatin jiha, shugaban ma’aikata da umurnin su tabbatar an bi wannan ka’ida.
Ya ce, “Gwamnati ba za ta lamunci almubazzaranci da karkatar da dukiyar gwamnati wajen yin zagon kasa ga kokarinmu na samar da ayyuka ga jama’a ba.”
Ya kuma umurci dukkanin manyan sakatarorin da su kasance ‘yan kasa nagari, su yi aiki tare da kwamishinoninsu da daraktoci da sauran ma’aikata a ma’aikatu da sassansu domin cimma burin da aka sa gaba domin samun sakamako mai ma’ana.
A cewarsa, ana sa ran a matsayinsu na jigo a tafiyar da ayyukan gwamnti, za su bai wa maras da kunya wajen nuna kwazo da bajinta da kwarewarsu domin cimma burin da aka sanya a gaba, da kuma gudanar da ayyukan da ake bukata cikin inganci ga al’ummar jihar.
“Kwanan nan gwamnatinmu ta dauki sama da mutum 2,600 da suka kammala digiri, babbar difloma da karamar difloma da NCE aiki domin cike gurbi a ma’aikatan gwamnati wajen bunkasa ayyukan yi.”
“Duk hanyoyin sadarwa da kai-komo na fayal-fayal dole ne su bi kai’idoji da tsare-tsaren da suka dace. Saboda bai kamata a rika sakin fayal-fayal din gwamnati ga mutanen da ka’idar aikin gwamnati bai ba su da izini ba. Na umurci sakataren gwamnatin jiha da ya lura kuma ya yi aiki yadda ya kamata kan haka.”