• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Ya Ƙaddamar Da Aikin Sake Gina Asibitin Talata Mafara

Za a samar da sashen da zai kunshi gadaje 200

by Leadership Hausa
1 year ago
Asibiti

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da aikin sake gina babban asibitin Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da samar da katafaren ginin da zai ɗauki gadaje 200.

A yayin ƙaddamarwar, gwamnan ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta kiwon lafiya a jihar, tare da bayyana irin rawar da manyan asibitoci ke takawa a fannin kiwon lafiya.

Mallam Yahaya Abdulkarim, tsohon gwamnan Jihar Sakkwato ne babban baƙo na musamman a wajen bikin ƙaddamarwar.

Gwamna Dauda Lawal, ya bayyana damuwarsa kan yadda aka yi watsi da babban asibitin Talatan Mafara, inda ya nuna cewa asibitin na fama da rashin isassun kayan aikin jinya da kuma rashin kyawun ababen more rayuwa a tsawon shekaru.

Ya ce gwamnatocin baya sun yi watsi da harkar kiwon lafiya gaba ɗaya, wanda hakan ya sa gwamnatinsa ta fara aiwatar da aikin gyara fannin.

LABARAI MASU NASABA

Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 

NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan

“Da yardar Allah yau na zo ne domin cika alƙawarin da na ɗauka a watannin baya lokacin da na ziyarci wannan asibiti da jami’ar jihar. Bisa la’akari da halin da ake ciki a wannan cibiyar kiwon lafiya, na yi alƙawarin gudanar da aikin sake gina shi gaba ɗaya don samar da babban asibitin da ya dace da babban gari kamar Talata Mafara.

“Gwamnatinmu ta ba da fifiko wajen farfaɗo da ababen more rayuwa a matsayin muhimmin ginshiƙin ajandar kawo sauyi. Mun sanya ilimi da kiwon lafiya a kan gaba, tare da sanin matsayinsu wajen ci gaban al’umma. Wannan asibiti ɗaya ne daga cikin wurare da yawa da ake ginawa don samar da yanayi mai kyau wajen samar da nagartaccen ayyukan kiwon lafiya.

  • Karin Kudin Mai: Hakika An Ci Amanarmu, In Ji ‘Yan Kwadago

 

“Gwamnatinmu ta tsaya tsayin daka wajen sanya hannun jari a fannin kiwon lafiya, tare da fahimtar muhimmiyar rawar da manyan asibitocin ke takawa a tsarin samar da lafiya. Suna aiki a matsayin muhimman hanyoyin da suka haɗa cibiyoyin Kula da Lafiya na Farko da Manyan Cibiyoyin Kiwon Lafiya.

“Aikin da muke ƙaddamarwa a yau ya ƙunshi gina asibiti mai ɗaukar gadaje 200 tare da samar da kayan aiki na zamani domin inganta lafiyar al’umma.

“Ya haɗa da gine-gine kamar haka: Wuraren zaman jira, sashin bayanai da asusun ajiya, sashen kula da yara, ɗakin jinya na maza, ɗakin jinya na mazan da aka yi wa tiyata, ɗakin gwaje-gwaje, ɗakin tiyata, ɗakin gwaje-gwajen haƙori, ɗakin karɓar magani, ɗakin jinya na matan da aka yi wa tiyata, ɗakin jinya na mata, sashen ENT. Ɗakunan haihuwa guda biyu tare da ofishin babbar mai karɓar haihuwa, ɗakin wankin ciwo, ɗakin zaman ma’aikatan jinya, ofishin Babban Manajan Daraktan Kiwon Lafiya na asibitin tare da ofishin sakatarensa, ofishin likitan haƙori, ɗakin canja kaya na mata, ɗakunan ganin likita guda biyar, ɗakin ICU, rukunin na’urar X-ray, sashen kai marasa lafiya na gaggawa ‘Accident & Emergency (A&E)’, sashen kula da masu juna biyu, wurin cin abinci, da ofishin matron.

“Za a kammala shi cikin watanni shida, inda kamfanin Abdulwahab Razaq Memorial Ltd ya kasance a matsayin ɗan kwangilar. A halin da ake ciki, abin farin ciki ne na musamman na gayyato babban baƙon mu, mai girma tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Malam Yahaya Abdulkarim, Magajin Rafin Sokoto, domin ƙaddamar da aikin gina wannan asibiti a hukumance.”

Tun da farko, tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Malam Yahaya Abdulkarim, ya yaba wa gwamna Dauda Lawal bisa bai wa ɓangaren kiwon lafiya fifiko a cikin ayyukan da gwamnatinsa ta sa gaba. “Na yi mamakin lokacin da gwamnan ya shaida min cewa an riga an sayo dukkan kayan aikin da za a yi amfani da su a Babban Asibitin, wannan abin yabawa ne matuƙa.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

2023: Gwarazan Jam’iyyu A Karon Battar Zaben Shugaban Kasa
Manyan Labarai

Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 

November 3, 2025
Likitoci
Labarai

NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan

November 3, 2025
Kano
Manyan Labarai

Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

November 3, 2025
Next Post
Rushewar Gine-gine Ta Yi Sanadiyar Rasuwar Mutane Fiye Da 90 A Shekara Daya

Rushewar Gine-gine Ta Yi Sanadiyar Rasuwar Mutane Fiye Da 90 A Shekara Daya

LABARAI MASU NASABA

2023: Gwarazan Jam’iyyu A Karon Battar Zaben Shugaban Kasa

Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso 

November 3, 2025
Likitoci

NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan

November 3, 2025
Kano

Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi

November 3, 2025
Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.