• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben Fidda Gwani: Gwamna Dauda Ya Ayyana Ighodalo A Matsayin Ɗan Takardar PDP A Zaɓen Jihar Edo

by Leadership Hausa
2 years ago
gwamna

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jagoranci zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar PDP a zaɓen Gwamnan jihar Edo da ke tafe.

A zaɓen da ya gudana yau Alhamis a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke garin Benin, Asue Ighodalo ne ya zama zakara, wanda ke nuni da cewa shi ne zai yi wa jam’iyyar takara a Edo.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Abuja, ya bayyana cewa zaɓen ya gudana cikin tsari da kwanciyar hankali, inda aka zaɓi wanda zai yi wa jam’iyyar PDP takara a zaɓen Gwamnan da ke tafe cikin watan Satumba mai zuwa.

  • Hukumar Kwastom Ta Fara Sayarwa ‘Yan Nijeriya Kayan Abincin Da Ta Kwace A Legas

Tun farko a jawabin sa kafin a fara zaɓen, Gwamna Dauda Lawal ya hori ‘yan takarar da su yi amanna da tsarin zaɓen, inda ya ba su tabbacin za a gudanar da zaɓe mai cike da adalci.

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

“Ko yanzu za ku iya gani, an yi tsari mai kyau buɗaɗɗe. Za mu gudanar da zaɓe na gaskiya mai inganci don samar da ɗan takara ga jam’iyyar mu a jihar Edo.”

Sanarwar ta Malam Idris ta ce, bayan kammala zaɓe da ƙirgawa, Gwamna Dauda Lawal, a matsayinsa na Baturen zaɓe, ya bayyana Ighodalo a matsayin gwanin da aka fitar bayan ya samu ƙuri’u 577, wanda ya doke sauran ‘yan takarar su tara.

“A matsayina na jagoran gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar PDP, na bayyana Asuelimen Ighodalo a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri’u 577.

“Ina taya shi murna, tare da yin kira ga sauran ‘yan takarar da su karɓi wannan sakamako da zuciya ɗaya. Wajibin mu ne mu haɗa kai mu dumfari yaƙi na gaba, zaɓen Gwamna.

“Wajibin mu ne mu sanya buƙatun jam’iyya birbishin buƙatunmu. Yanzu muna da ɗan takara, dolen mu mu bayar da cikakken goyon bayanmu,” In ji Gwamna Dauda.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure
Manyan Labarai

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista
Labarai

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio
Labarai

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025
Next Post
Sake Dawowar Matsalar Tsaro

A Tona Asirin Kungiyoyin Addinin Da Ke Daukar Nauyin Ta’addanci

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

November 5, 2025
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025
An Nemi Kasashen ECOWAS Su Samar Da Kariya Ga Yankunan Hakar Ma’adanai

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Sanata Barau Ya Tsaya Takarar Shugaban Majalisar Dattawa

Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio

November 5, 2025
CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

November 5, 2025
Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.