Yayin da Kiristocin Jihar Gombe ke bin sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da bukukuwan Kirsimeti na bana, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bukace su da dabbaka dabi’un kauna, sadaukarwa da kuma hakuri kamar yadda koyarwa Yesu Almasihu ya horar da su.
A sakonsa na taya murna dauke da sanya hannun Ismaila Uba Misilli, babban daraktan yada labara gwamnan, ya bukaci mabiya addinin Kirista a jihar da ma daukacin al’ummar Nijeriya baki daya da su ci gaba da karfafa imaninsu da Allah, tare da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.
- Adadin Kudin Da Kowacce Kasa Ta Samu A Gasar Cin Kofin Duniya
- Shugaban Kasar Equatorial Guinea: Kasashen Yamma Sun Yayata Furucin Wai “Sin Na Kafa Tarkon Bashi” A Yunkurin Su Na Dakile Kasar
Ya kuma bukaci jama’a su sake sadaukar da kan su ga addu’o’i, abin da ya ce yana da matukar tasiri ga zaman lafiya da hadin kan al’umma.
Gwamnan ya bayyana cewa “A wannan muhimmin biki na Kirsimeti, ina mika sakon fatan alheri ga al’ummar Kirista da daukacin al’ummar kasar nan.
“Wannan lokacin yana tunatar da mu bukatar dabbaka kyawawan halaye na kauna, sadaukarwa da kuma hakuri.
“Ina kira a gare mu duka, mu yi tunani a kan darusan wannan lokaci ke koyarwa da suka hada da kauna da soyayya da kuma kyauta.”
Da ya ke tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bullo da tsare-tsare da manufofin da za su inganta hadin kai da zaman lafiya a jihar.
Gwamnan ya bukaci jama’ar jihar su yi amfani da wannan lokacin wajen yi wa jihar da kasa addu’ar zaman lafiya da ci gaba don gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.
“Ina kira a gare ku, ku yi amfani da wannan lokaci wajen sadaukar da kai cikin addu’o’i ga Allah Madaukakin Sarki don ya dawo mana da zaman lafiya a cikin al’ummarmu, mu yi addu’ar Allah Ya dawo mana da zaman lafiya.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar kar su yanke kauna, su ci gaba da kasancewa da bege duk da irin kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da duniya ke ciki, wadda cutar Korona da yakin Rasha da Ukraine da kuma rashin tsaro da ake fama da shi a Nijeriya suka haifar.