Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, a cikin watanni 17 na gwamnatin ta, ta sasanta rikicin da suka shafi filayen noma 347 cikin lumana, sai kuma ta ware wasu filaye 203 don musanya wa wasu da ke rikicin.
Babban Darakta Janar na Hukumar kula da filaye ta Kaduna (KADGIS), Dokta Bashir Garba Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a karshen mako.
- Birtaniya Ta Bukaci ‘Yan Kasarta Su Gaggauta Ficewa Daga Lebanon
- Hanyoyi 13 Na Ladabtar Da Mata Ba Tare Da Duka Ko Zagi Ba
Dokta Ibrahim ya ce, a matsayin hanyar kauce wa rigima a nan gaba, Gwamna Sani ya bullo da wani sabon tsari na tantance filaye da ake da su wajen samar da sabbin filaye.
Ya bayyana cewa, gwamnan ya amince da rage kudade da kuma ka’idojin daidaitawa don saukaka mallakar filaye a wannan yanayi na kalubalen tattalin arziki da ake ciki.
Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar Kaduna tana zamanantarwa tare da inganta ayyukan KADGIS domin gaggauta samar da takardun shaidar mallakar muhalli 200 a duk mako.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp