Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya sanar da rage kudaden manyan makarantu da dalibai ke biya a jihar da kashi 30 da 50 cikin 100.
A wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Muhammad Lawal Shehu ya fitar, ya bayyana cewa, bayan sake bitar kudaden makarantun, sabon tsarin zai kama kamar haka:
Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta samu ragin kashi 30 daga Naira N150,000 zuwa N105,000.
Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli ta samu ragin kashi 50, daga Naira N100,000 zuwa N50,000.
Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya, ta samu ragin kashi 50, daga Naira N75,000 zuwa N37,500.
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Shehu Idris, Makarfi ta samu ragin kashi 30, (HND) daga Naira N100,000 zuwa N70.000, yayin da (ND) za su biya Naira N52,000 maimakon Naira N70,000 da ake biya a baya.
Kwalejin Jinya ta Jihar Kaduna, ta samu ragin kashi 30, daga Naira N100,000 zuwa N70,000.
A cewar sanarwar, wannan bitar na rage kudaden makarantun na daga cikin kudirin Gwamnan na cika alkawuran da ya yi wa al’ummar jihar Kaduna a lokacin yakin neman zabensa.