Yayin da gwamnatin ke hangen cika kwanaki 100 a kan karagar mulki, Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da karin nade-naden mukamai domin aiwatar da shirin manufar gwamnatinsa.
Sabbin mukaman da aka nada a bangarori daban-daban na gwamnatin, ga su kamar haka:
- Umar Waziri – Mashawarci na Musamman kan tattara kudin shiga.
- Umar Baba Bambale – Mashawarci na Musamman kan harkar Magunguna
- Farfesa Aminu Ladan Sharehu – Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikata ta Kananan Hukumomi.
- Arc. Abubakar Rabiu Abubakar – Manajan Darakta na Kamfanin Kula da Kaddarorin Jihar Kaduna (KSDPC)
- Hadiza Yahaya Hamza – Manajan Darakta, ta Kamfani mai kula da masana’antu da harkokin kudi ta Jihar Kaduna.
- Engr. Inuwa Ibrahim – Manajan Darakta, mai kula da tashar motocin sufuri ta jihar Kaduna.
- Dr Iliyasu Neyu – Babban Sakatare na Hukumar Yaki da cutar kanjamau ta Jihar Kaduna (KADSACA).
- Dr Usman Abubakar – Darakta Janar na Hukumar Tabbatar da ingancin kayayyaki na jihar Kaduna (KSSQAA).
- Dr Bello Jamo – Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko na Jiha (SPHCB).
- Joseph O. Ike – Babban Sakatare, Ofishin Kariya da Magance zubar da shara na Jihar Kaduna (KADBUSA).
- Mohammed Rili – Babban Manaja na Hukumar Raya Aikin Gona ta Jihar Kaduna (KADA).
- Rakiya A. Umar – Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Nakasassu ta Jihar Kaduna
- Usman Hayatu Mazadu – Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA).
- Muhammed Mu’azu Mukaddas – Babban Manaja, Hukumar Cigaban Al’umma da Zamantakewa.
- Dr Jamilu Haruna – Mamba na Dindindin, a majalisar kula da Ilimi ta matakin farko a jihar Kaduna (SUBEB)
- Maryam Abubakar – Babbar Darakta a Kamfanin da ke kula da kadarori da habbaka su na jihar Kaduna (KSDPC).
Yayin da yake taya sabbin wadanda aka nada, Gwamna Sani ya bukace su da su yi nuna kwarewarsu ta hanyar samar da tsare-tsare da za su amfani al’ummar jihar Kaduna. Ya kara da cewa dole ne su yiwa al’ummar jihar Kaduna hidima da kwazo da da’a da gaskiya.