• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Umar Namadi Ya Dauki Matakan Kai Jihar Jigawa Babban Matsayi

by Rabi'u Ali Indabawa
6 months ago
Jigawa

Gwamna Umar Namadi, FCA wanda Jaridar LEADERSHIP ta karrama shi a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2024, hakika ya nuna kwarewa duba da irin rawar da ya taka tun bayan da ya karbi ragamar jagorancin jihar a shekarar 2023.

Salon shugabancinsa irin wanda ba a saba ganinsa ba wajen samar da romon dimokradiyya ga jihar a kowane fanni ya cancanci a yaba masa.

  • An Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Cambodia
  • Ina Da Ƙwarewar Da Zan Iya Zama Shugaban Ƙasar Nijeriya – Makinde

Bayan rantsar da shi a shekarar 2023 nan take ya aiwatar da kyawawan manufofi da azamar sauya wa jihar fasali ta fuskar karfafa wa matasa da mata, ta fannin inganta Ilimi, lafiya, Noma, da ababen more rayuwa na bukatu da dama da saka baza a sassan jihar domin kowa ya amfana.

Daya daga cikin wadannan manufofi na kawo sauyi da ya aiwatar kasa da watanni uku da shigarsa ofis sun hada da, kafa Hukumar Samar Da Ayyukan Yi ga Matasa ta Jihar Jigawa wato (YEEA), domin magance kalubalen rashin aikin yi a jihar.

Wannan hukumar ta bude wani shafin Intanet da ya yadu a jihar domin matasa su rika dora bayanansu wajen nemo matasa marasa aikin yi a jihar.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

A cikin dan kankanin lokacin da wannan hukuma ta fara aiki, ta horar da matasa sama da 100,000 horo kan shirye-shiryen koyon sana’o’i daban-daban a fannonin noma, ICT, kananan sana’o’i da dai sauran su, gwamnatin jihar ta bayar da tallafi da jarin sama da Naira biliyan 1.7 ga wadannan matasa domin fara sana’o’i. Har ila yau, ya saukaka wa wadannan matasa rayuwa sa suka cancanta a cikin jihohi da tarayya.

Jihar jigawa jiha ce mai girma ta kuma yi fice a fannin noma a kokarin gwamnati na inganta rayuwar al’umma ta hanyar sabbin manufofin noma da ya zama abin a yaba.

Domin tabbatar da samar da wadataccen kayan aikin noma akai-akai, gwamnatin jihar ta zuba Naira biliyan 5 ga kamfanin samar da aikin gona na Jihar Jigawa (JASCO).

Haka zalika, Gwamnatin Namadi ta samar da sabbin tsare-tsare a fannin noma ta hanyar inganta tsarin samar da shinkafa, alkama, sesame da hibiscus domin bunkasa yankunan jihar.

A tsawon lokacin da ake bitar, jihar ta sayi tan 9,200 na taki, tarakta 60, tare da motocin girbi 10 gami da samar da fili mai fadin hekta 40,000 don shirin noman alkama wanda ya zama hadin gwiwa ne da gwamnatin tarayya.

Gwamnatin jihar ta kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna MOU da Bankin Duniya, Bankin Raya Afirka da Bankin Raya Musulunci a fannin noma da dai sauransu.

Haka kuma ayyukan da gwamnatin Namadi ta yi a fannin ilimi ba boyayye ba ne.

Shi ne Gwamna daya tilo a Nijeriya da ya zarce shawarar da UNESCO ta bayar na samar da kaso 25 a kasafin kudi ta fannin ilimi, wanda wannan shi ne karon farko da aka samu a tarinhin Jihar Jigawa da watakila a Arewacin Nijeriya.

Sannan Gwamna Namadi ya ware kashi 32 na kasafin kudi wa fannin ilimi, wanda ba kasafai ake samu ba a Nijeriya. Ya kara wa dalibai tallafin karatu da kashi 100 yayin da ya kara kudin ciyar da dalibai da kashi 40 cikin 100.

Har ila yau, gwamnatinsa ta dauki dalibai 150 da suka kammala karatun digiri na farko a jihar a matsayin malamai a manyan makarantun jihar yayin da aka bai wa malamai 3,570 aikin yi a makarantun firamare da sakandare a fadin jihar ta hanyar shirin J-Teach. haka kuma gwamnati ta gina manyan makarantun sakandare a jihar .

Domin magance matsalar yara da ba sa zuwa makaranta, gwamnatin ta bullo da sabbin makarantu na Mega Tsangaya tare da cibiyoyin ilimi da fasaha na yammacin Turai don magance wannan matsalar.

Jihar ta kuma hada gwiwa da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta Nijeriya NITDA, domin horo gami da zurfafa ilimin malaman Jigawa da basu kwarewa ta fasahar sadarwa ICT saboda bunkasa fasaharsu ta koyarwa.

Bugu da kari, a fannin lafiya an samu sauye-sauye da dama a wannan bangare da ya shafi ma’aikatan lafiya a jihar inda aka fitar da Naira biliyan 17.2 domin kammala ayyukan asibitoci daban-daban a fadin jihar.

Gwamnatin ta kuma fitar da asusun kula da lafiya na Naira biliyan 1.2 domin kafa tsarin kiwon lafiya na Inshora ga gidaje sama da 140,000 tare da mutane 500 da suka cancanta a dukkan gundumomi 287 da ke fadin jihar.

Gwamnatin jihar ta shirya gina Cibiyar Kula da Lafiya a Matakin Farko a kowace Unguwa da kuma Babban Asibiti daya a kowace mazaba.

Gwamna Namadi ya kuma jajirce wajen tunkarar kalubalen da talakawa da marasa galihu ke fuskanta a cikin al’umma. Ya sanya an gudanar da kidayar gidajen marayu, nakasassu, tsofaffi da sauran su domin taimaka musu, sannan ya kara alawus din Tsaron Jama’a daga Naira 7000 zuwa 10,000.

Wani bangare na rangadin da Gwamnan ya fara a duk fadin yankin mazabu shi ne, jin ta bakin talakawa kai tsaye domin samar da mafita mai dorewa ga marasa galihu a cikin al’ummarmu.

Haka kuma gwamna ya sake samar da wasu tsare-tsare a fannin lafiya domin saukaka wa majinyata masu fama da cutuka masu tsanani kamar su ciwon koda, ciwon daji da kuma hanta a jihar ta hanyar biyan kudaden majinyatan da suka jima da larurar domin ganin sun warke daga cutar.

A kasa da shekaru biyu, Gwamna Namadi ya nuna kwarewa, iya aiki da kuma jajircewa wajen inganta rayuwar al’ummar jihar kuma sakamakon hakan ne yake ta samun lambobin yabo na karramawa a fadin kasar nan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Next Post
Xi: Daukar Matsayar Kashin Kai Da Danniya Ba Za Su Taba Samun Goyon Bayan Al’umma Ba

Xi: Daukar Matsayar Kashin Kai Da Danniya Ba Za Su Taba Samun Goyon Bayan Al’umma Ba

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Asuu

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.