Sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar na zaben Gwamna da ya gudana a jihar Borno, ya bayyana Babagana Umara Zulum na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna da ya gudana ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023.
Da yake ayyana sakamakon da yammacin yau Litinin, babban jami’in hukumar INEC (Returning Officer), Jude Rabo, ya ce dan takarar jam’iyyar APC, Babagana Zulum shi ne ya samu nasarar lashe zaben da kuri’u 545,542.
Bugu da kari kuma, yayin da babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Mohammed Jajari ya samu adadin kuri’u 82,147.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp