Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya dakatar da Sarkin Lame da ke ƙaramar hukumar Toro a jihar, Mai Martaba Alhaji Aliyu Yakubu Lame, daga jagorantar harkokin masarautar bisa zargin aikata ba daidai ba.
Gwamnan ya kuma amince da kafa kwamitin mai mambobi 12 domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa basaraken, inda aka ba kwamitin wa’adin makonni uku domin gabatar da rahotonsa da shawarwarinsa ga gwamnati.
Gwamnatin jihar ta ce matakin ya biyo bayan samun ƙorafe-ƙorafe da dama, da kuma rahotannin sirri daga shugabannin al’umma, masu ruwa da tsaki da hukumomin tsaro kan zargin amfani da muƙaminsa ta hanyar da ba ta dace ba, yin amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba da sauran halaye da ake ganin sun saɓa da nauyin da ke kan mai sarautar gargajiya.
Zarge-zargen da ake yi wa Sarkin sun haɗa da tsoma baki ba bisa ƙa’ida ba a harkokin kula da filaye, karɓar kuɗaɗen haraji ko wasu kuɗaɗe ba tare da izini ba, tsoma baki fiye da kima a ayyukan kamfanonin haƙar ma’adinai, da sauran abubuwan da ake zargin sun saɓa wa ƙa’ida.
Gwamnatin ta ce waɗannan abubuwa sun haifar da rahotannin tashin hankali a masarautar Lame, tare da janyo damuwa kan yiwuwar barazana ga zaman lafiya, tsaro da kyakkyawar zamantakewa a yankin.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar ranar Juma’a, ya ce ma’aikatar ƙananan hukumomi da harkokin Masarautu ta buƙaci Sarkin da ya yi bayani a hukumance kan zarge-zargen da ake yi masa, bisa bin ƙa’idojin adalci da bai wa kowa damar kare kansa.
Sanarwar ta ce duk da cewa Sarkin ya gabatar da rubutaccen bayaninsa, gwamnati ba ta gamsu da bayanan da ya bayar ba, don haka ta ga buƙatar gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa domin gano haƙiƙanin gaskiya da kuma samar da shawarwarin da suka dace.
Sai dai gwamnatin ta jaddada cewa zarge-zargen da ake yi wa Sarkin na nan a matsayin zarge-zarge da ake buƙatar gudanar da bincike a kansu, kuma za a ba shi cikakkiyar damar kare kansa kan dukkan zarge-zargen da ake masa bisa bin doka da ƙa’idojin adalci.
Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Mohammed ya yi amfani da ikon da dokar naɗawa da sauƙe sarakunan gargajiya ta Jihar Bauchi ta shekarar 2026 ta ba shi wajen amincewa da kafa kwamitin binciken mai mambobi 12.
Kwamitin ya ƙunshi Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yansanda mai ritaya, DIG Sani Mohammed, a matsayin shugaba.
Sauran mambobin sun haɗa da Musa Mohammed Yankari, tsohon Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), da wakilan kwamishinan ‘Yansanda, Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC), Ma’aikatar Shari’a, Ma’aikatar Muhalli da Ma’aikatar Bunƙasa Albarkatun Kasa.
Sauran sun hada da wakilan Shugaban ƙaramar Hukumar Toro, Hukumar Kula da Ma’aikatan ƙananan Hukumomi da Daraktan Harkokin Sarautun Gargajiya na Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu.
Daraktan Gudanarwa da Albarkatun Ma’aikata na Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu ne zai zama sakataren kwamitin.
Ana sa ran kwamitin zai gudanar da cikakken bincike cikin adalci da zaman kansa, ta hanyar nazarin korafe-korafe, takardu da sauran hujjoji da suka dace, gayyatar wadanda abin ya shafa, tare da bai wa Sarkin damar kare kansa kafin mika rahotonsa da shawarwarinsa ga gwamnati cikin makonni uku.
Sanarwar ta kuma tabbatar da dakatar da Sarkin daga gudanar da aikinsa nan take har zuwa lokacin kammala binciken kwamitin.
Gwamnatin ta bayyana cewa dakatarwar wani mataki ne na gudanarwa na wucin gadi domin kare sahihancin binciken, hana yiwuwar katsalandan ga shaidu da takardun hukuma na masarautar, tare da rage tashin hankalin da ka iya tasowa a cikin al’umma.
A tsawon lokacin dakatarwar, an umarci Sarkin da ya kasance a cikin masarautar Lame, sai dai idan wata hukuma mai hurumi ta ba shi izinin fita. Haka kuma, an hana shi tsoma baki a harkokin gudanarwa, na sarauta da sauran ayyukan Majalisar Masarautar Lame.
Domin tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin masarautar ba tare da tangarda ba, gwamnati ta umarci Alhaji Bala Abubakar Gumau, Galadiman Lame, da ya kula da harkokin gudanarwa na yau da kullum a matsayin wanda zai riƙe ragamar masarautar na wucin gadi har zuwa kammala binciken da kuma samun ƙarin umarni daga gwamnati.
Gwamnatin jihar ta yi kira ga al’ummar masarautar Lame, shugabannin al’umma, masu riƙe da sarautun gargajiya, matasa da sauran masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankulansu, su zauna lafiya, su kiyaye doka da oda, tare da ba jami’an tsaro da kwamitin bincike hadin kai a tsawon lokacin gudanar da binciken.
Gwamnatin ta sake jaddada kudirinta na kare martaba, mutunci, sahihanci da kuma tabbatar da rikon amana a cikin tsarin sarautun gargajiya a fadin jihar.
Idan za a iya tunawa, a ranar 25 ga Oktoba, 2025, Gwamna Bala Mohammed ya miƙa takardar naɗin sarauta a hukumance ga Alhaji Aliyu Yakubu Lame, inda aka tabbatar da shi a matsayin Sarkin Lame na farko Mai daraja ta biyu, bayan ƙirƙirar sabbin masarautu 13 a Jihar Bauchi.














