Shugaban jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) na ƙasa, Yusuf Mamman Dantalle, ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta shiga takarar zaɓe ne kawai domin samun kujerun siyasa ba, sai dai domin dawo wa ’yan Nijeriya ikon siyasa da ’yancin zaɓen waɗanda za su shugabance su a dukkan matakai.
Dantalle ya ce jam’iyyar na neman mayar da ikon gudanar da harkokin siyasa hannun al’umma ba wai ɗauki ɗaura da wasu jam’iyyun ke yi ba.
Tana mai jaddada buƙatar sake fasalta tsarin dimokuraɗiyyar Nijeriya, wadda ya bayyana da cewa tana ƙara fuskantar takura da barazana a karkashin mulkin APC ta shugaban Bola Tinubu.
Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Bauchi, yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APM gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
A cewarsa, dimokuraɗiyyar Nijeriya ba ta taɓa kasancewa cikin irin wannan mawuyacin hali ba kamar yanzu.
Don haka ne ya ce APM ta yi wani sabon tsari da zai kyautata dimokuraɗiyya, shugabanci, bunƙasa tattalin arziki da inganta walwalar al’umma.
Shugaban APM ya ce matsalolin zamantakewa da tattalin arzikin da ke addabar ƙasar, musamman rashin tsaro, talauci da fatara su na nuna manyan matsaloli da ke cikin tsarin siyasa, zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya.
Ya nuna damuwarsa kan hauhawar farashin man fetur, yana mai cewa farashin ya ƙara zama abin da talakawan Nijeriya ba za su iya biya ba, duk da muhimmancin da mai ke da shi a rayuwar yau da kullum.
Dantalle ya tambayi dalilin da ya sa ake ci gaba da ƙara farashin man fetur, yana mai cewa bayanan da ake bayarwa kan hauhawar farashin ba su dace da haƙiƙanin halin tattalin arziki da kuma ƙarfin samun kuɗin talakawan ƙasar ba.
Ya kuma bayyana cewa manufofin gwamnati da ke hana ’yan ƙasa samun muhimman buƙatun rayuwa na iya kawo cikas ga ƙoƙarin yaƙi da cin hanci da rashawa.
Ya ce, “Ba za ku iya yaƙi da cin hanci da rashawa yadda ya kamata ba, alhali manufofin da kuke aiwatarwa suna hana ’yan ƙasa samun muhimman buƙatun rayuwarsu da abubuwan da suke buƙata domin tsira.”
A cewarsa, rashin daidaito tsakanin albashi da tsadar rayuwa ya haifar da mawuyacin yanayin tattalin arziki wanda ka iya jefa wasu ’yan ƙasa cikin halin matsananciyar buƙata.
Ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar yunwa da matsin tattalin arziki na iya ƙarfafa aikata laifuffuka, ciki har da sata, fashi da makami da garkuwa da mutane, yayin da mutane ke ƙoƙarin neman abin da za su rayu da shi.
Dantalle ya kuma nuna damuwarsa kan yadda halin tattalin arzikin da ake ciki ya jefa wasu mutane, har ma da waɗanda ake sa ran za su riƙa kula da iyalansu, cikin aikata laifuffuka.
Dantalle ya buƙaci ’yan Nijeriya da su mara wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Injiniya Seyi Makinde, da mataimakinsa, Daura, baya a babban zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa jam’iyyar na gabatar da wani sabon tsari na magance matsalolin tsaro, tattalin arziki da shugabanci da ke addabar ƙasar.













