Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), Injiniya Seyi Makinde, ya buƙaci ’yan Nijeriya da cewa a duk lokacin da ‘yan jam’iyyar APC suka ba su kuɗaɗe a yayin yaƙin neman zaɓen 2027 su amsa, amma kuma kada su zaɓi jam’iyyar.
Ya ce, koda sun yi wa jama’a tayin kudaden, mutane su yi amfani da hankalinsu wajen zaɓin ‘yan takaran da suka dace domin tabbatar da bada nasarar ceto ƙasar nan daga halin da take ciki na mayuwacin halin rayuwa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Bauchi, yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, inda ya gargaɗi masu zaɓe da kada su bari kuɗin da ’yan siyasa ke bayarwa ya rinjayi ra’ayinsu.
Makinde ya ce bai kamata ’yan Nijeriya su ƙi karɓar kuɗin da ’yan siyasa za su ba su a lokacin yaƙin neman zaɓe ba, yana mai jaddada cewa kuɗin na al’umma ne, amma hakan bai kamata ya sa su sauya ra’ayinsu ko ƙin zaɓin ɗan takarar da suke goyon baya ba.
Ya ce, “Idan suka zo da kuɗi lokacin zaɓe, kada ku damu, kada ku ƙi karɓa. Daman kuɗin naku ne, ku karɓa ku kashe. Amma ku adana ra’ayinku, sannan ku yanke shawara mai kyau idan lokacin zaɓe ya yi. Na san zukatanku suna tare da mu, kuma su na tare da ni.”
Ɗan takarar shugaban ƙasar na APM ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya waɗanda ba su gamsu da halin da ƙasar ke ciki ba, musamman matsalar rashin tsaro, yunwa da gazawar gwamnati wajen magance manyan ƙalubalen da ke addabar ƙasar, da su mara wa jam’iyyarsa baya.
Ya ce, “Idan ba ku farin ciki da halin da ƙasarmu ke ciki a yau, musamman ƙaruwa da matsalar rashin tsaro, yunwa da gazawar gwamnati wajen magance ƙalubalen da ’yan Nijeriya ke fuskanta, to akwai jam’iyya guda ɗaya da ya kamata mu mara wa baya. Wannan jam’iyyar ita ce jam’iyyar da ke mutunta Nijeriya.”
Makinde ya buƙaci ’yan Nijeriya da su rungumi tafiyar siyasar APM, inda ya bayyana magoya bayan jam’iyyar da sunan “Resetters”, wato masu son sauyi da sabunta tsarin mulki.
Ya ce jam’iyyar APM ta duƙufa wajen mutunta al’ummomi, ƙarfafa tsarin tsaro na ƙasa da samar da yanayin siyasa da zamantakewa wanda zai ba wa ’yan Nijeriya dama su taka rawar gani a harkokin mulki.
Ɗan takarar shugaban ƙasar ya yabawa uban jam’iyyar na ƙasa kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, bisa karɓar baƙuncin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen.
Ya kuma nuna godiyarsa ga shugaban jam’iyyar APM na ƙasa bisa ba shi damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar, domin gabatar da hangen nesansa na yi wa ’yan Nijeriya hidima.
Makinde ya ce jam’iyyar APM ta ƙuduri aniyar samar wa ’yan Nijeriya wata sabuwar hanya ta siyasa wadda za ta iya magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta.














