Gwamnan Jihar Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, Bala Mohammed, ya ce jam’iyyar ta gaji da rikice-rikicen da wasu ‘yan tsagi ke janyo mata.
Ya yi wannan magana ne bayan ɓangaren Nyesom Wike ya sanya wasu sharuɗa kafin a gudanar da babban taron jam’iyyar na ƙasa.
- Sabuwar Ajandar Mulkin Duniya Ta Nuna Alhakin Da Kasar Sin Ta Dauka
- Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita
Sharuɗan sun haɗa da:
- Shugaban jam’iyya dole ya fito daga Arewa ta Tsakiya.
- A sake zaɓen shugabannin jam’iyya a Ebonyi da Anambra.
- A amince da sakamakon zaɓen shugabannin Kudu maso Kudu da aka yi a Calabar.
- A sake zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Ekiti ba tare da jinkiri ba.
Sai dai a martaninsa, Bala Mohammed ya ce shugabannin PDP mutane ne da suka san darajar jam’iyya, ba za su bari a riƙa yi musu wasa da hankali ba.
Ya ƙara da cewa shugaban jam’iyya na ƙasa ya riga ya yi magana a fili, kuma babu wani shakku game da kwamitin da ke shirya taron, domin sun taɓa yin hakan a baya, kuma suna da tabbacin za su yi nasara.
Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp