Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, a ranar Litinin ya kaddamar da shimfida hanya mai nisan kilomita 19 da ta tashi daga garin Liman Katagum ta nufi garin Luda zuwa Lekka da ke cikin karamar hukumar Bauchi.
Aikin wanda zai lakume naira Biliyan N2,400,000,000 zai gudana ne bisa hadin guiwa da babban bankin duniya ta karkashin shirin bunkasa hanyoyin karkara (RAAMP).
Da ya ke kaddamar da aikin, gwamna Bala Muhammad, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da inganta rayuwar al’ummar karkara ta hanyoyi daban-daban musamman na samar musu da hanyoyin tituna da za su hadesu da sauran al’ummomi domin bunkasa harkokin kasuwancinsu da hada-hadar yau da gobe.
A cewarsa, nan ba da jimawa ba, gwamnatinsa za ta cigaba da shimfida ayyukan titina da dama domin kara saukaka wa matafiya da kuma bunkasa harkokin tattalin arziki a sassan jihar.
Bala ya yi amfani da damar wajen jinjina wa kokarin babban bankin duniya, ya kuma gargadi dan kwangilar da aka ba shi aikin da ya tabbatar da ya yi aiki mai nagarta da inganci, yana mai cewa da kansa zai ke bibiyar aiki domin tabbatar da an yi mai inganci.
Gwamnan, ya ce, da zarar aka kammala aikin hanyar Liman Katagum-Luda-Lekka, zai kawo karshen matsalolin da manoma suke fuskanta na fitar da amfanin gonarsu na tsawon shekaru, kuma a cewarsa, hakan zai taimaka wajen bunkasa kiwon lafiya, harkokin ilimi, jin dadi da walwalar al’umman yankin.
Tun da farko a jawabinsa, kwamishinan ayyukan musamman da raya yankunan karkara na jihar Bauchi, Hon. Farouk Mustapha, ya ce, bayan kammala aikin hanyar, hanyar za ta hade al’ummomin Liman Katagum, Luda da Lekka hadi da sauran kauyukan da ke yankunan kuma za a samu bunkasar tattalin arziki.
Faruk ya ce, ana sa ran karkashin shirin RAAMP jihar Bauchi za ta ci gajiyar hanyoyi da nisansu ya kai na kilimiya sama da dubu a sassa daban-daban.
A nata bangaren, shugaban riko na karamar hukumar Bauchi, Hajiya Zainab Baban Tanko, ta nuna matukar godiyarta ne ga gwamnan bisa tsayuwar dakar da yake yi wajen ganin ya kyautata rayuwar al’ummar jiha da na karkara.
Ta nuna cewa, tsawon lokaci al’ummar wannan yankin suna bukatar wannan hanyar don haka ta nuna farin cikin da al’umman ke ciki dangane da fara aikin hanyar.
Ta bukaci al’umman yankin da su bayar da hadin kai domin cimma nasarar aikin a daidai lokacin da aka tsara.
Shi kuma a nasa bigiren, Ko’odinetan shirin RAAMP, Injiniya Aminu Muhammad Bodinga, ya ce, jihar Bauchi na daga cikin jihohi 19 da za su amfana da shirin bayan cika ka’idojin da shirin ke bukata.